Bayan Harin Amurka a Sokoto, Sojoji Sun Dura Fadar Sarkin Musulmi

Bayan Harin Amurka a Sokoto, Sojoji Sun Dura Fadar Sarkin Musulmi

  • Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya kai ziyarar girmamawa ga Sarkin Musulmi a Sokoto domin ƙarfafa dangantakar soji da al’umma
  • Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da rundunar sojin ke ƙara jajircewa wajen haɗin gwiwa da shugabannin gargajiya don samar da zaman lafiya
  • A gefe guda kuma, manyan hafsoshin tsaro sun gana da dakarun Operation Fansan Yamma domin ƙarfafa musu guiwa a lokacin bukukuwan Kirsimeti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto – Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, CFR, a fadarsa da ke jihar Sokoto.

An gudanar da ziyarar ne a ranar 26, Disamba, 2025, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin rundunar sojin ƙasa na ƙarfafa alaƙa da shugabannin gargajiya wajen tallafa wa zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Kara karanta wannan

An kama kasurgumin 'dan bindiga mai nuna miliyoyin kudi a intanet

Sarkin Musulmi tare da shugaban sojin kasan Najeriya
Sarkin Musulmi tare da Laftanar Janar Waidi Shuaibu. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai kan ziyarar ne a wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na dandalin Facebook.

Sojoji sun ziyarci Sarkin Musulmi

A yayin ziyarar ga Sarkin Musulmi, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya jaddada aniyar rundunar sojin ƙasa ta ci gaba da aiki tare da shugabannin al’umma da na gargajiya domin inganta zaman lafiya da zaman tare.

Ya bayyana cewa shugabannin gargajiya na da matuƙar muhimmanci wajen isar da saƙonni na zaman lafiya da haɗin kai ga al’umma, musamman a yankunan da ke fuskantar ƙalubalen tsaro.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yaba da irin sadaukarwar da rundunar sojin ƙasa ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da yin addu’ar Allah Ya ba su nasara a ayyukansu.

Manyan sojoji sun ziyarci Sokoto

Kafin ziyarar ga Sarkin Musulmi, Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, tare da Babban Hafsan Sojin Ƙasa, sun kai ziyara ga dakarun Operation Fansan Yamma a sansanin Giginya da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya girgiza kan mutuwar 'yan majalisar Kano 2 a lokaci guda

A ranar 26, Disamba, 2025, manyan hafsoshin sun shirya wata liyafar Kirsimeti ta musamman domin ƙarfafa gwiwar dakarun da ke bakin aiki a yankin Arewa maso Yamma.

Janar Oluyede ya yabawa dakarun bisa jarumtaka, ladabi da jajircewarsu wajen kare ƙasa, yana mai jaddada cewa sadaukarwarsu ta taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali da amincewar jama’a a yankin.

Za a kula da walwalar sojojin Najeriya

Babban Hafsan Tsaro ya tabbatar wa dakarun cewa jin daɗinsu na daga cikin manyan abubuwan da rundunar ke bai wa fifiko, ciki har da inganta yanayin rayuwa, kula da lafiya da tallafa wa iyalan jami’ai.

Ya kuma yi gargadin cewa lokutan bukukuwa na iya zama damar da masu aikata laifuffuka ke ƙoƙarin amfani da su, don haka ya buƙaci dakarun su kasance cikin shiri tare da bin ƙa’idojin aiki da kare haƙƙin ɗan Adam.

Sojojin Najeriya a jihar Sokoto
Lokacin da manyan sojoji suka isa Sokoto. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A nasa jawabin, Laftanar Janar Waidi Shaibu ya bayyana liyafar Kirsimeti a matsayin al’ada da ke nuna godiya ga jajircewa da ƙwarewar dakarun da ke ayyukan tsaro.

Gwamnatin Sokoto ta yi bayani kan harin Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Sokoto ta yi bayani game da harin da sojojin Amurka suka kai jihar bisa umarnin Donald Trump.

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto

Gwamnatin Ahmed Aliyu ta tabbatar da kai harin tare da karin bayani da cewa babu wani da aka kashe ko ji wa rauni a Sokoto.

Ta kara da cewa za ta goyi bayan duk wani kokarin kawo zaman lafiya da magance matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar a bisa tsarin doka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng