Rashin Tsaro: Shugaba Tinubu Ya Nemi Daukin Kasar Waje bayan Amurka
- Gwamnatin tarayya na ci gaba da kokarin ganin ta shawo kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar nan
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya za ta karbi odar jiragen yaki guda hudu da ta yi daga kasar Amurka
- Hakazalika, ya bayyana cewa Najeriya ta nemi taimako daga wajen kasar Turkiyya kan matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta ce ta nemi taimako kan matsalar rashin tsaro.
Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta nemi taimakon kasar Turkiyya domin magance kalubalen rashin tsaro da ke addabar Najeriya a halin yanzu.

Source: Facebook
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ganawa da wata tawagar Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) kamar yadda Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.
Mai girma Tinubu ya gana da tawagar kungiyar CAN ne karkashin jagorancin shugabanta, Archbishop Daniel Okoh, a gidansa da ke Legas.
Bola Tinubu ya bukaci goyon-bayan CAN
Shugaban kasar ya bukaci CAN da ta hada kai da gwamnatinsa domin cimma burin da ’yan Najeriya ke da shi baki daya, yana mai cewa wasu daga cikin matakan da gwamnatinsa ta dauka na bukatar lokaci kafin su fara yin tasiri.
“Yanayin kasar nan yana cikin kwanciyar hankali, duk da cewa akwai manyan yankuna da ba sa karkashin mulki. Kalubalen yana nan, amma za mu yi nasara a kansa."
"Mu mutane ne masu addini. Mu masu yawan addu’a ne. Muna bukatar hankalinku, sa ido da hadin kai."
“’Yan sandan al’umma da na jihohi za su zama fara aiki da zarar majalisar tarayya ta kammala tanade-tanaden doka da ake bukata. Kayan aikin soja kuwa ba su da saukin maye gurbinsu, suna da tsada kuma ba sa samuwa kai tsaye.”
- Shugaba Bola Tinubu
Wace kasa Tinubu ya nemi taimakonta?
Shugaba Tinubu ya ce odar jiragen yakin sama guda hudu da aka yi daga Amurka za su dauki lokaci kafin su iso, inda ya kara da cewa:
“Mun kuma nemi taimako daga kasar Turkiyya.”
Sai dai shugaban ya amince cewa jinkirin da ake fuskanta na shafar yadda jama’a ke kallon jajircewar gwamnatinsa wajen magance matsalolin tsaro.

Source: Twitter
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta sassauta ba wajen kokarinta na dawo da zaman lafiya da wadata a kasar nan, duk da dabarun farmaki na ’yan bindiga da ’yan ta’adda.
Wannan ci gaban ya biyo bayan hadin gwiwa da aka samu a baya-bayan nan tsakanin Gwamnatin Tarayya da Amurka wajen yakar rashin tsaro da tayar da kayar baya a kasar.
Tinubu ya amince da harin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da amincewarsa kafin harin da Amurka ta kawo kan 'yan ta'adda.
Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta taɓa yarda da duk wani abu da zai take ikon ƙasar ba.
Hakazalika, ya bayyana cewa Najeriya ce ta ba da bayanan sirri da aka yi amfani da su wajen kawo harin a jihar Sokoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

