Babban Limami Ya Fito Ya Gayawa Tinubu Gaskiya kan Mulkin Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da hutun karshen shekara da yaje yi a jihar Legas da Kudancin Najeriya
- Mai girma Bola Tinubu ya halarci sallar Juma'a tare da wasu mukarraban gwamnatinsa a babban Masallacin Lekki
- Limamin masallacin ya yi wa shugaban kasar nasiha a cikin hudubar da ya gabatar kafin gudanar da sallar Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shugaba Bola Tinubu ya halarci sallar Juma’a tare da al’ummar Musulmi a Masallacin Lekki Central da ke jihar Legas a ranar Juma’a, 26 ga watan Disamban 2025.
Limamin masallacin ya tunatar da Shugaba Tinubu cewa ba zai iya gamsar da kowa ba a lokaci guda.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar.
Wace shawara aka ba Tinubu?
A cikin hudubar da ya gabatar, limamin masallacin, Dakta Salahudeen Munirudeen Arriyadhi, ya yaba wa Shugaba Tinubu kan dimbin ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Ya karfafa masa gwiwar ya ci gaba da jajircewa duk da kalubale da kuma sukar da ake yi masa, jaridar The Punch ta dauko labarin.
“Ba za ka iya gamsar da kowa a lokaci guda ba."
- Dakta Salahudeen Munirudeen Arriyadh
Limami ya yi nasiha ga Tinubu
A cewar sanarwar, Dakta Arriyadhi wanda ya ambato ayoyin Alkur'ani, ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa Allah yana farin ciki da shugabannin da ke sauraron koke-koken al’ummarsu, amma ba ya jin dadin shugabannin da ba sa kula da bukatun wadanda suke jagoranta.
“Muna yi maka addu’a, kuma za ka yi nasara."
- Dakta Salahudeen Munirudeen Arriyadh
A hudubar da ya yi, Dakta Arriyadhi ya ce bambancin dan Adam ta fuskar launi, kabila, addini, harshe da kasa ba a banza ya faru ba, illa tsari ne da nufin Allah.

Kara karanta wannan
Abin da gwamnoni 19 suka ce kan bam din da ya tashi a masallacin Juma'a a Maiduguri
Ya kara da cewa bambanci bai kamata ya zama barazana ba, sai dai tushen jituwa, hadin kai da koyon darussa a tsakanin mutane.
“Bambanci alama ce ta hikimar Allah. Da Allah Ya so dukkannin halittunsa su zama daya, da Ya halicce su haka. Bambancin addini da kabila bai kamata ya zama sanadin matsala ba."
- Dakta Salahudeen Munirudeen Arriyadh

Source: Twitter
Tinubu ya je tare da mukarrabansa
Shugaba Tinubu ya halarci sallar ne tare da shugaban ma’aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, da wasu manyan jami’ai.
Ya samu tarba daga wajen mataimakin gwamnan jihar Legas, Dakta Obafemi Hamzat, da shugabanni masu kula da masallacin.
Shugaba Tinubu ya isa jihar Legas a ranar Asabar, 20 ga Disamba, domin yin hutun karshen shekarar a birnin kasuwanci mafi girma a kasar.
Atiku ya taso Tinubu a gaba
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargi kanShugaba Bola Tinubu.
Atiku ya zargi Shugaba Tinubu da kin aiwatar da hukuncin Kotun Koli kan 'yancin kananan hukumomi.
Ya ce rashin aiwatar da hukuncin wata dabara ce ta siyasa da aka tsara domin amfani da bin doka a matsayin makami na matsa wa gwamnonin adawa su koma jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng
