Sharudan da Tinubu Ya Bayar kafin Harin Amurka kan ’Yan Ta’adda a Sokoto

Sharudan da Tinubu Ya Bayar kafin Harin Amurka kan ’Yan Ta’adda a Sokoto

  • Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da hare-haren Amrurka a Sokoto
  • Ambasada Tuggar ya ce Najeriya ce ta bayar da bayanan sirri ga Amurka, kuma an yi aikin ne tare, ba tare da take yancin ƙasar ba
  • Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa hare-haren ba su da alaƙa da addini, illa yaki da ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta yi martani game da harin kasar Amurka kan sansanin 'yan ta'adda da aka y a jihar Sokoto.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ne ya amince da hare-haren sama da sojojin Amurka suka kai kan sansanonin ’yan ta’adda.

Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da harin Amurka a Sokoto
Shugaba Donald Trump da Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Donald J Trump, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta tabbatar da harin Amurka

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a 26 ga watan Disambar 2025 yayin hira da Channels TV.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda daga ketare na 'shirin' kawo hari jihohin Arewa 4 a Najeriya

Hirar na zuwa ne awanni kaɗan bayan Ma’aikatar Yaƙin Amurka da Shugaba Donald Trump sun sanar da kai harin na haɗin gwiwa.

Tuggar ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta taɓa yarda da duk wani abu da zai take ikon ƙasar ba.

Tuggar ya ce:

“Haɗin gwiwa ne, kuma wannan shi ne abin da muke ta kira."
“Najeriya ce ta bayar da bayanan sirri da aka yi amfani da su wajen harin. Na tattauna da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, na tsawon mintuna 19 kafin harin, sannan muka amince za a nemi izinin Shugaba Tinubu, wanda ya bayar.”
Minista ya fadi sharadin Tinubu ga Amurka kafin kai hari Sokoto
Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar da Donald Trump. Hoto: Yusuf Maitama Tuggar, Donald J Trump.
Source: Facebook

Abin da Tinubu ya yi kafin harin

Tuggar ya ƙara da cewa bayan samun amincewar shugaban ƙasa, ya sake magana da Marco Rubio mintuna biyar kacal kafin a kaddamar da harin kan ’yan ta’addan.

“Yanzu da Amurka ta fara ba da haɗin kai, za mu gudanar da aikin ne tare, kuma za mu tabbatar, kamar yadda shugaban ƙasa ya jaddada jiya kafin ya bayar da izini cewa a fayyace cewa aikin haɗin gwiwa ne, ba kai hari kan wani addini ba, ko a madadin wani addini ɗaya ba.”

Kara karanta wannan

Rawar da sojojin Najeriya suka taka yayin harin Amurka a Sokoto

- Yusuf Tuggar

Premium Times ta ruwaito cewa harin na haɗin gwiwar Amurka da Najeriya ya shafi sansanonin ’yan ta’adda da ke jihar Sokoto.

Hare-haren sun shafi ’yan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar ISIS/ISWAP, waɗanda ake zargi da kai hare-haren bama-bamai da farmaki kan fararen hula a yankin.

An bayyana cewa hare-haren sun samo asali ne daga samun bayanan sirri da haɗin kai na dabarun tsaro tsakanin Rundunar Sojin Amurka a Afirka da sojojin Najeriya.

Ko da yake ba a bayyana adadin waɗanda suka mutu ba, jami’an Amurka sun ce an kai hare-haren ne kan muhimman wuraren ’yan ta’adda.

Tuggar ya ce Najeriya ƙasa ce mai addinai da dama, kuma tana aiki da ƙawayenta kamar Amurka domin yakar ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mazauna Sokoto sun koka kan harin Amurka

Kun ji cewa Amurka ta tabbatar da kai wani hari kan yan ta'adda a jihar Sokoto a daren jiya Alhamis 25 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya aika sako ga Tinubu bayan harin Amurka a Sakkwato

Mazauna kauyen Jabo a Tambuwal a jihar Sokoto sun shiga tsananin fargaba bayan Amurka ta kai harin bama-bamai.

Wani ganau ya ce karar fashewar makaman ta girgiza gidaje, yayin da jami’an tsaro suka garzaya wurin da abin ya watse.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.