"Yadda Muka Ji Saukar Harin Amurka': Mazaunin Sakkwato
- Mazauna Jabo a karamar hukumar Tambuwal sun ce sun tsinci kansu a cikin tsoro da fargaba bayan faduwa 'bam' da Amurka ta jefa masu
- Wani mazaunin yankin, Abubakar Umar Jabo ya tabbatar wa da Legit cewa da farko sun dauka jirgi ne ya fado, amma suka tarar da akasin haka
- Ya ce a daren Juma'a ne bayan jama'a suna kokarin su shiga gida domin su kwanta barci, sai suka ji kara da haske mai karfin gaske a sama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Mazauna jihar Sokoto, musamman a garin Jabo da ke karamar hukumar Tambuwal, sun bayyana yadda suka ji saukar abin da Amurka ta ce ta jefa a yankin, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.
Wani mazaunin yankin, Abubakar Umar Jabo, ya shaida wa Legit cewa suna zaune ne lokacin da suka ji kara mai karfi, wacce ya ce ta yi kama da saukar jirgi daga sama da farko.

Source: UGC
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a daren Juma’a ne Amurka ta kai harin a Najeriya, amma rahotanni sun nuna cewa babu wanda ya jikkata sakamakon harin.
Sakkwato: Yadda jama'a suka ji harin Amurka
Abubakar Jabo ya tabbatar wa Legit cewa bayan sun ji kara da ke kara kusanto su, saii kowa ya fita waje domin ganin abin da ke faruwa.
A kalamansa:
“Ina zaune a majalisa, na taso na shigo cikin gida, to shigowata cikin ke nan ke da wuya sai muka ji karar wannan abin. Karar shi duk wanda zai ji shi, zai ce kamar jirgi ne na sama yake saukowa. To sai muka fito da sauri domin ka ji menene zai zo. Don idan ka shiga cikin daki, za ka ji kamar a saman dakinka ne abin zai fado. Da muka fito, sai muka tsinkayi haske. Hasken da muka tsinkaya, duk jin shi da karar shi bai wuce dakika biyar ba. Sai ka dauka ma bayan gidanka ne.”
Ya kara da cewa:
“Allah ya sa bai fado cikin gari ba, ya fadi nan bayan gari. Gidajen da ke kusa da wurin, akwai kauyuka da ake kira Sakanau da Barkini, kauyuka ne a mazabar Jabo. Tsakiyarsu ne abin ya faru.”
Wuta ta tashi bayan faduwar abin
Abubakar Jabo ya ce bayan faduwar abin, sai ya yi rami a inda ya fado, tare da tayar da wuta mai tsananin zafi da suka yi fargabar ko yana bin kasa ne.
A cewarsa:
“Wutar ta kai kimanin awa daya da rabi tana ci. Bayan lokacin da abin ya rage ne, mutane suka yi kokari suka je wurin tare da jami’an soja, suna hana mutane zuwa kusa da wurin saboda ba a san me zai iya faruwa ba.”

Source: Original
Ya ce sun shiga fargaba ganin yadda kasa ta kama da wuta mai tsanani, wacce ya ce ba su taba ganin irinta ba, lamarin da ya sa suka ji tsoron kada abin da aka jefa yana ci gaba da yawo a cikin kasa.
Mazaunin yankin Jabo ya kara da cewa:
“Mu gaskiya bakon abu ne a gare mu, ba mu taba ganin irin wannan ba. Sannan kuma babu inda ‘yan ta’adda suke da mafaka ko suke da wurin zama a inda wannan abu ya faru.”
Ya ce akwai tazara mai nisa tsakanin yankinsu da wuraren da ‘yan ta’adda ke kai hare-hare ko sace mutane domin neman kudin fansa.
A karshe, ya yi addu’ar kada irin wannan lamari ya sake faruwa, musamman ganin cewa an kai harin a yankin da ba a san shi da matsalar ta’addanci ba.
Amurka ta kai hari Najeriya
A wani labarin, mun wallafa cewa gwamnatin Amurka ta sanar da kaddamar da hare-haren sama kan wasu wurare da ake zargin ‘yan ta’addar ISIS ke amfani da su a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce shi ne ya bayar da umarnin kai hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin hare-hare masu ƙarfi da hadari ga ‘yan ta’adda don kare rayukan kiristoci.
Wannan ne karo na farko da sojojin Amurka suka kai irin wannan hari a Najeriya tun bayan da Donald Trump ya sake komawa kan karagar mulki, kuma harin na zuwa ne bayan barazanar Amurka.
Asali: Legit.ng


