Rawar da Sojojin Najeriya Suka Taka yayin Harin Amurka a Sokoto
- Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana matsayarta game da harin kasar Amurka a jihar Sokoto a ranar Alhamis
- Sojojin sun tabbatar da hadin gwiwa da Amurka wajen kai hare-haren sama kan ‘yan ta’addan ISIS ‘yan kasashen waje a Arewa maso Yamma
- Sojoji sun ce an kai harin ne bayan sahihin bayanan sirri, da tsauraran tsare-tsare, domin rage karfin ‘yan ta’adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar Sojin Najeriya ta magantu kan hadin da kasar Amurka ta kai a jiya Alhamis 25 ga watan Disambar 2025.
Rundunar tare da hadin gwiwar kasar Amurka, ta kai hare-haren sama kan wasu ‘yan ta’addan ISIS ‘yan kasashen waje a Arewa maso Yamma.

Source: Twitter
Martanin sojojin Najeriya kan harin Amurka
Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'a 26 ga watan Disambar 2025 a Abuja, cewar Premium Times.
Ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun amincewar hukumomin da suka dace, a matsayin wani bangare na yaki da ta’addanci da aikata laifuka.
Uba ya ce harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da tsauraran shirye-shiryen aiki, domin raunana karfin ‘yan ta’adda tare da rage illa ga fararen hula.
Sanarwar ta ce:
"Rundunar Sojin Najeriya, tare da haɗin gwiwar ƙasar Amurka, ta yi nasarar kai sahihan hare-haren sama kan wasu ‘yan ta’addan ISIS ‘yan ƙasashen waje da ke aiki a wasu a Arewa maso Yammacin Najeriya.
“Hare-haren sun biyo bayan sahihan bayanan sirri da tsauraran tsare-tsaren aiki, domin raunana ƙarfin ayyukan ‘yan ta’addan tare da rage illar da ka iya shafar fararen hula.
“An gudanar da aikin ne bisa bayanan sirri masu amfani da kuma cikakken shiri, inda aka tsara shi musamman don kawar da waɗanda aka nufa tare da kauce wa illata fararen hula.”

Source: Facebook
Kokarin da sojoji ke yi kan ta'addanci
Uba ya bayyana cewa aikin ya nuna kudurin gwamnatin tarayya, tare da kawayenta na kasa da kasa, na dakile ta’addanci da hana ‘yan waje kafa sansani a Najeriya.
Sojojin Najeriya sun sake jaddada aniyarsu ta kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, tare da ci gaba da hadin gwiwa domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Ya bukaci yan Najeriya su ci gaba da ba da bayanan sirri da duk wasu hanyoyin taimakawa sojoji domin tabbatar da karar da yan bindiga, cewar Vanguard.
Harin Sokoto: Amurka ta gode wa Najeriya
A baya, mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Amurka ta yi magana bayan harin da ta kai kan sansanin yan ta'adda a jihar Sokoto.
Ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya gode wa gwamnatin Najeriya bisa hadin kai yayin hare-haren sama da aka kai kan ’yan ta’adda.
Amurka ta ce harin ya biyo bayan gargadin Donald Trump kan kisan fararen hula, inda ta jaddada cewa ma’aikatar tsaro a shirye take koyaushe.
Asali: Legit.ng

