Kwankwaso Ya Gabatar da Sama da Masu Digirin PhD 300 da Kwankwasiyya Ta Horar
- Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ilimi shi ne abin da ya fi dorewa a cikin al'umma
- Ya bayyana haka ne a yayin taya wasu dalibai 300 da gidauniyar Kwankwasiyya ta kyankyashe da digirin digirgir a Kano
- Kwankwaso ya bukaci masanan su yi hidima ga al'ummarsu tun daga ƙananun matakai domin a more su a rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ya bayyana sama da masu digirin digirgir wato PhD 300 a jihar.
Wadannan mutane na daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu da gidauniyar Kwankwasiyya ta samar domin inganta ilimi a tsakanin mabiya tafiyar siyasar Kwankwaso.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa tsohon Ministan ya bayyana daliban ne a taron farko na shekara-shekara na masanan Kwankwasiyya da aka gudanar a Kano.
Rabiu Kwankwaso ya jaddada amfanin ilimi
The Guardian ta ruwaito Kwankwaso ya jaddada cewa ilimi shi ne gadon da ya fi kowane abu dorewa da shugaba zai iya ba wa al’umma.
Tsohon Gwamnan ya bayyana cewa ci gaba da zuba jari a harkar ilimin dan adam shi ne ma’aunin shugabanci nagari.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin sanarwar da Dr Mansur Hassan, shugaban kungiyar Kwankwasiyya 'Scholars Assembly' na kasa, ya fitar a Kaduna.
Da yake jawabi a taron wanda ya hada wadanda suka amfana da shirin tallafin karatu tsawon kusan shekaru 25, Kwankwaso ya bayyana taron a matsayin wani abin tarihi ga Kano da Najeriya baki daya.
Ya ce:
“Ina tuna da da yawa daga cikinku tun kuna kanana. Wasu ma kamar daga kauyuka ku ka fito kai tsaye. Yau kuma na ga kwarewarku har ma da furfura."

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya fadawa Tinubu tsarin da zai yi kan tsaro idan ya samu mulkin Najeriya
Fatan Sanata Kwankwaso ga masanan Kwankwasiyya
Jagoran na Kwankwasiyya ya ce taron ya koyar da darussa masu muhimmanci kan shugabanci, dorewa da hangen nesa, yana mai jaddada cewa ya kamata a rika auna mulki da tasirinsa na dogon lokaci a rayuwar jama’a.
Kwankwaso ya bayyana cewa bayan zaben 2019, lokacin da aka dakatar da tallafin gwamnati ga daliban da ke karatu a kasashen waje, ya yanke shawarar ci gaba da shirin da kansa ta hanyar gidauniyar Kwankwasiyya.
Ya ce:
“Na fahimci ina da kadarori da ba na bukata—filaye a Legas, Kaduna, Sakkwato, Adamawa da wasu wurare. Na sayar da su duka, na kuma dauki kudin na tallafa wa matasa 370 daga Kano su yi karatu a kasashen waje."
Kwankwaso ya kara da cewa kafin wannan lokaci, shirin tallafin ya dauki sama da dalibai 3,000 cikin shekaru hudu, inda suka yi karatu a kasashe 14 a Turai, Asiya, Afrika da Gabas ta Tsakiya.
A cewarsa, shirin ya samar da daruruwan likitoci, matuka jiragen sama, injiniyoyi, masana fasahohi, da malamai masu bincike, ciki har da sama da masu PhD 300.

Source: Facebook
Ya ce manufar gidauniyar ba wai tallafin karatu kadai ba ne, har da bibiyar wadanda suka ci gajiyar shirin, ba su shawarwari, da shigar da su harkokin mulki da ci gaban kasa.
Kwankwaso ya gargadi malamai da su guji nuna girman kai, yana cewa samun digirin PhD bai kamata ya hana yin hidima a matakin kasa ba.
Ya yaba wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa nada wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin a mukaman kwamishinoni da masu ba da shawara.
Madugun siyasar ya yi masu fatan wasu daga cikinsu za su zama gwamna, wasu kuma su zama Shugaban Ƙasa nan gaba.
Kwankwaso ya yi gargadi game da tsaro
A baya, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan matsalolin tsaro.
Kwankwaso, wanda ya taba rike mukamin ministan tsaro, ya jaddada cewa ‘yan daba, ta’addanci, rikicin kabilanci da yaduwar makamai suna kara zama babban barazana ga jama'a.
Kwankwaso ya ce daya daga cikin alamu na gazawar gwamnati shine yadda ake bari wasu jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da samun cikakken horo kan gudanar da aiki ba.
Asali: Legit.ng

