Aminu Ado Ya Jajanta Rasuwar ’Yan Majalisar Kano 2, Ya Tura Sako ga Abba Kabir
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya nuna matuƙar alhini kan rasuwar ‘yan majalisar Kano guda biyu
- 'Yan majalisar da suka rasu, Aminu Sa’ad Ungogo da Sarki Aliyu Daneji, sun wakilci Ungogo da birnin Kano, inda suka yi aiki da kishin jama’a.
- Sarkin ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu, ya ba iyalansu haƙuri, tare da miƙa ta’aziyya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Majalisar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya fitar da sanarwa bayan rasa yan majalisun Kano biyu.
Basaraken ya bayyana kaɗuwa da bakin ciki kan rasuwar ‘yan majalisar bayan gajerar jinya da suka yi fama da ita.

Source: Twitter
Aminu Ado ya jajanta kan rasuwar 'yan majalisa
Hakan na cikin wata sanarwa da Alhaji Aminu Babba Dan-agundi ya sanyawa hannu wanda shafin Masarautar Kano ta wallafa a Facebook.
Sarkin ya ce rasuwar Hon. Aminu Sa’ad Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji babban rashi ne, yana mai yabawa jajircewarsu wajen hidimtawa jama’a.
"Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana matuƙar kaɗuwa da jimami kan rasuwar mambobi biyu na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Aminu Sa’ad Ungogo (Ungogo) da Hon. Sarki Aliyu Daneji (Kano), waɗanda suka rasu ranar 24 ga Disamba, 2025 bayan gajeriyar jinya.
"Sarkin ya bayyana rasuwar ‘yan majalisar biyu a jere a matsayin babban rashi mai raɗaɗi ga Jihar Kano, yana mai jaddada cewa dukkaninsu sun yi wa mazabunsu da al’umma hidima da jajircewa, kishi da kuma mulki nagari."

Source: Facebook
Ta'aziyyar Aminu Ado Bayero ga Abba Kabir
Basaraken ya miƙa ta’aziyya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, Majalisar Kano da iyalai, yana addu’ar Allah ya gafarta musu ya ba al’umma haƙuri.
Aminu Ado ya yi addu'a Ubangiji ya gafarta musu kura-kuransu, ya karbi kyawawan ayyukansu tare da saka musu da aljannar firdausi.
"A madadin Majalisar Masarautar Kano da daukacin al’ummar Kano, Sarkin ya miƙa ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, dukkan ‘yan majalisar, iyalan mamatan, da kuma al’ummar Ungogo da birnin Kano.
"Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta kura-kuransu, ya karɓi ayyukan alherinsu, ya ba su Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano haƙuri da juriyar wannan rashi."
Abba Kabir ya kadu da rasuwar 'yan majalisa
An ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa rasuwar 'yan Majalisar dokokin Kano guda biyu ta jefa shi cikin kaduwa.
A wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Gwamna Abba ya mika sakon ta'aziyya ga majalisar dokokin Kano da al'ummar Ungoggo da birnin Kano.
Ya ce wannan rasuwa ta jajirtattun mutane masu kaunar jama'a jarabawa ce mai radadi, inda ya bukaci al'ummar Kano su zama masu hakuri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

