Barau Jibrin Ya Tuna Alherin Ganduje a Kano da APC, Ya Yi Masa Addu’o’i

Barau Jibrin Ya Tuna Alherin Ganduje a Kano da APC, Ya Yi Masa Addu’o’i

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yabawa gudunmawar Abdullahi Umar Ganduje a Najeriya
  • Barau Jibrin ya tuna irin gudunmawar tsohon shugaban APC ga jam'iyyar da kuma jihar Kano yayin mulkinsa
  • Ya bayyana Ganduje a matsayin jagora mai hangen nesa wanda ya taka rawar gani wajen ci gaban Jihar Kano da kuma haɗa kan APC a matakin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yabawa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Barau ya taya tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje, murnar zagayowar ranar haihuwarsa bayan cika shekaru 76 a duniya.

Barau ya taya Ganduje murnar cika shekaru 76
Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: @barauijibrin.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da sanatan ya yi a shafinsa na X a jiya Alhamis 25 ga watan Disambar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan

Kano: Barau ya zargi Abba da take hakkin Alfindiki, ya ba shi kudin da aka hana shi

Barau ya yaba gudunmawar Ganduja a Kano, APC

A cikin rubutun, Barau ya yabawa rawar da Ganduje ya taka a matsayin mataimakin gwamna, gwamna da shugaban APC wajen haɗa jam’iyya da samun nasarori.

Ya tuna tasiri da hidimar da Ganduje ya yi lokacin da yake mataimakin gwamnan Kano daga shekarun 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.

Har ila yau, Barau bai manta da gudunmawar Ganduje ba bayan ya zama gwamnan daga 2015 zuwa shekarar 2023 musamman wurin ci gaba Kano kafin karbar ragamar shugabancin APC.

A cikin rubutunsa, Barau ya ce:

"Ina taya tsohon Shugaban Jam’iyyarmu mai girma ta APC ta ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, Khadimul Islam, murnar cika shekaru 76 a duniya.
"A matsayinsa na mataimakin gwamna (1999–2003 da 2011–2015) da kuma gwamnan Jihar Kano (2015–2023), ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban jiharmu.
"Haka kuma, shugabancinsa mai hangen nesa a matsayin Shugaban APC na ƙasa (2023–2025) ya ƙarfafa haɗin kai, tare da taimakawa jam’iyyar samun nasarori a wasu zaɓukan cike gurbi."

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Barau Jibrin ya yi wa Ganduje addu'o'i bayan cika shekaru 76
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

Addu'o'i da Barau ya yi wa Ganduje

Sanata Barau ya yi wa Ganduje ruwan addu'o'i inda ya roki Ubangiji ya kara masa lafiya da kariya domin ci gaba da hidima ga al'umma.

Ya roƙi Allah ya ƙara masa karfin guiwa, shiriya saboda ya ci gaba da yi wa Najeriya da al’umma hidima kamar yadda ya saba.

"Allah SWT ya ci gaba da ba shi lafiya, shiriya da kariya, domin ya ci gaba da hidimtawa ƙasarmu da al’umma baki ɗaya.
"Barka da cika shekaru 76, Ranka ya dade."

- Sanata Barau Jibrin

Barau ya zargi Abba Kabir da take hakki

Kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya mika Naira miliyan 7 ga tsohon shugaban karamar hukuma a jihar Kano, Fa’izu Alfindiki yayin da ya ziyarce shi a Abuja.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce an riƙe kudin ne tsawon lokaci saboda tsayuwarsa kan gaskiya da goyon bayan jam’iyyar APC.

Duk da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya hakkin tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Kano, ana zargin ba a biya Alfindiki kudinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.