Sojojin Amurka Sun Kawo Hari Najeriya don 'Kare Rayukan Kiristoci'

Sojojin Amurka Sun Kawo Hari Najeriya don 'Kare Rayukan Kiristoci'

  • Kasar Amurka ta ce ta kai hare-hare kan yan ta'adda da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ne bisa bukatar gwamnati
  • Harin ya auku a Arewa maso Yammacin kasar, a yankin jihar Sakkwato inda jama'a suka ji ƙarar da ta girgiza wasu gidaje
  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kai harin ne bayan gargaɗin cewa hakan za ta faru idan ba a daina kashe kiristoci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Gwamnatin Amurka ta sanar da kaddamar da hare-haren sama kan wasu wuraren da ake zargin ‘yan ta’addar ISIS suna amfani da su a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya bayar da umarnin kai hare-haren, yana mai bayyana su a matsayin masu karfi da kuma hadari ga ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Najeriya ta ce game da harin Amurka a Sakkwato

Amurka ta kawo hari Najeriya
Shugaban Amurka Donald Trump, jirgin yakin Amurka Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da Ma'aikatar yaƙi ta Amurka ta fitar, sannan ya wallafa a shafinta na X a daren Juma'a.

Kasar Amurka ta kawo hari Najeriya

DW ta wallafa cewa wannan ne karo na farko da sojojin Amurka suka kai irin wannan hari a Najeriya tun bayan Trump ya sake komawa kan karagar mulki.

Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun gudana ne a wasu sassan jihar Sakkwato, inda ake zargin ‘yan ta’adda ke fakewa suna kai hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro.

Rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afrika, AFRICOM, ta bayyana cewa an kai hare-haren ne bisa bukatar hukumomin Najeriya.

Rundunar ta ce an yi aikin cikin tsari da nufin rage barazanar tsaro a yankin da dakile kashe kiristoci a Najeriya.

Amurka ta godewa Gwamnatin Najeriya

Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin Najeriya, yana cewa hadin kai da bayanan sirri da aka samu daga hukumomin kasar sun taimaka matuka wajen nasarar aikin.

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya kaddamar da sababbin dabaru na kawo karshen ƴan bindiga a Sokoto

A nata bangaren, Ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta tabbatar da kai hare-haren, tana mai cewa an yi ingantattun hare-hare kan wuraren ‘yan ta’adda.

Amurka ta godewa Najeriya bayan kawo hari kasar
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Amurka Donald Trump
Source: Twitter

Ma’aikatar ta jaddada cewa gwamnatin Najeriya tana daukar kare rayukan dukkanin ‘yan kasa a matsayin babban nauyi, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Sanarwar da ma’aikatar ta ce ta’addanci da ake yi wa kowace al’umma abin Allah-wadai ne, kuma barazana ce ga zaman lafiya da tsaron kasa da ma duniya baki daya.

A wani sako da ya fitar, Trump ya ce dalilin kai harin shi ne abin da ya kira hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa kan fararen hula, musamman Kiristoci.

Shugaban Kasar Amurka ya ce ba zai bari “tsattsauran ra’ayin addini” ya yi katutu a karkashin shugabancinsa ba.

Amurka ta jawo wa Najeriya asara

A baya, mun wallafa cewa Najeriya ta fuskanci gagarumar asara a bangaren kasuwancin waje, musamman wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar Amurka, bayan dokar harajin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa wannan sabon tsari ya shafi kasashe da dama, ciki har da Najeriya, inda ya rage anfani da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje zuwa Amurka.

A sakamakon haka, kudin da Najeriya ke samu daga fitar da kayayyaki zuwa wannan kasa sun ragu sosai a shekarar 2025 kamar yadda binciken da hukumar Kkdiddiga ta kasa (NBS) ya nuna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng