Abin da Gwamnoni 19 Suka Ce kan Bam din da Ya Tashi a Masallacin Juma'a a Maiduguri
- Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai wani masallacin Juma'a a Maiduguri, jihar Borno
- Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce harin ya saba wa dabi'a ta dan adam
- Ya tabbatar wa al’ummar Borno cewa dukkan gwamnonin Arewa na tare da su, kuma suna goyon bayan kokarin da hukumomin tsaro ke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadai da harin kunar bakin wake da ya afku a Masallacin Kasuwar Gomboru da ke Maiduguri, Jihar Borno.
Kungiyar, wacce gwamnoni 19 ke karkashinta, ta bayyana harin a matsayin aikin ta’addanci, rashin imani da kuma zalunci da aka shirya domin tarwatsa zaman lafiya.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya fitar yau Alhamsi.
Gwamnoni 19 sun yi Allah wadai da harin bam
Ya bayyana matuƙar alhini da baƙin ciki kan lamarin, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin da al’ummar Jihar Borno, musamman Gwamna Babagana Umara Zulum, da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka jikkata.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce kai hari wurin ibada kamar masallaci ya saba wa ɗabi’ar ɗan Adam da tsarkin addini, yana mai jaddada cewa irin waɗannan munanan ayyuka ba za su karya ƙudurin dao da zaman lafiya a Arewa ba.
Ya kuma buƙaci jami’an tsaro da shugabannin gwamnati a Jihar Borno da kada su fidda rai ko su yarda da tsoratarwar da 'yan ta'adda ke kokarin yi ta hanyar irin wadannan hare-hare.
Matakan da gwamnoni auka nemi a dauka
Gwamnan ya yi kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren ibada da tarukan jama’a, musamman a lokutan bukukuwa da jama’a ke taruwa da yawa.
Ya tabbatar wa al’ummar Borno cewa dukkan gwamnonin Arewa na tare da su, kuma suna goyon bayan hukumomin tsaro a kokarin hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.

Source: Facebook
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya sanya su a Aljannatul Firdaus, Ya kuma bai wa iyalansu haƙuri, tare da bai wa waɗanda suka jikkata cikakkiyar lafiya.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya ba shugabannin Jihar Borno ƙarfi da hikima wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da jarumtaka da juriya, in ji Vanguard.
A ƙarshe, shugaban ƙungiyar ya jaddada ƙudurin gwamnonin Arewa na ci gaba da aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da kare rayukan fararen hula.
Shettima ya dauki zafi kan harin masallaci
A wani rahoton, kun ji cewa Kashim Shettima ya yi tir da harin na kunar bakin wake , wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane biyar tare da jikkata wasu da dama a Maiduguri.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya yi magana mai jan hankali kan tashin bam a wani Masallaci a Maiduguri
Mataimakin shugaban kasa ya ce wannan mummunan ibtila'i, hari ne kai tsaye ga zaman lafiya da tsaron ƙasa baki ɗaya, amma hakan ba zai dakatar da shirin mukushe ta'addanci ba.
Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin ƙara tsaurara ayyukan tsaro nan take a Jihar Borno.
Asali: Legit.ng

