Tinubu Ya Canza Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Fito

Tinubu Ya Canza Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Fito

  • Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin da ke yawo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire Femi Gbajabiamila daga mukaminsa
  • Rahoton da mutane ke yadawa a soshiyal midiya ya yi ikirarin cewa Tinubu ya maye gurbin Gbajabiamila da Hakeem Muri-Okunola
  • Bayo Onanuga ya ce labarin kanzon kurege ne, har yanzu Gbajabiamila nan nan kujerarsa ta shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wasu rahotanni da aka fara yadawa a soshiyal midiya sun yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Jita-jitar ta bayyana cewa Bola Tinubu ya tsige Gbajabiamila, ya kuma maye gurbinsa da babban sakatarensa, Hakeem Muri-Okunola.

Femi Gbajabiamila.
Bola Ahmed Tinubu tare da ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Fadar shugaban kasa ta fito ta karyata wannan labari da ake yadawa a wata sanarwa da mai magana a yawun shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura tawaga Morocco yayin da Najeriya za ta fafata da Tanzania a AFCON 2025

Dagaske Tinubu ya canza Gbajabiamila?

Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta, ta ce Shugaba Tinubu bai cire Gbajabiamila tare da dora Hakeem Muri-Okunola a mukamin ba.

A sanarwar da Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 25 ga Disamba, 2025, fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa labarin ƙarya ne tsantsa kuma babu wata gaskiya a cikinsa.

Sanarwar ta jaddada cewa Femi Gbajabiamila na nan a kan muƙaminsa a matsayin shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa.

Haka zalika Hakeem Muri-Okunola na nan yana ci gaba da aikinsa a matsayin babban sakataren tsare-tsare na shugaban kasa, Bola Tinubu.

Fadar shugaban kasa ya karyata labarin

Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce babu wani sauyi da aka yi, kuma babu wani shiri na sauya ɗaya daga cikinsu da ɗaya.

“Wannan labari da ke yawo a kafafen sada zumunta ƙirƙirarre ne, kuma wasu masu yaɗa labaran ƙarya ne suka kulla munafurcin domin haddasa ruɗani a cikin gwamnati,” in ji sanarwar.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta fallasa yadda aka so korar ta, ’ya’yanta daga fadar shugaban kasa

Femi Gbajabiamila.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

An bukaci 'yan Najeriya su yi fatali da jita-jitar

Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da jita-jitar gaba ɗaya, tare da jan kunnen kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da sahihancin labari kafin wallafawa ko yaɗawa.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da aikinta yadda ya kamata, ba tare da wata tangarda ko rikici a cikin tsarin gudanarwa ba.

Tinubu ya kafa kwamitin gudanarwa na NERC

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake kafa kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC.

Tinubu ya dauki wannan mataki ne bayan tantancewar da aka yi musu daga Majalisar Dattawa, ana sa ran wadanda aka nada za au ci gana da kokarin kawo sauyi a fannin wutar lantarki a kasar nan.

An nada Dr Mulisiu Olalekan Oseni, wanda ya fara aiki a NERC tun.shekarar 2017 a matsayin shugaban kwamitin daga ranar 1 ga Disamba, 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262