'Yan Bindiga Sun Kai Hari kan Shingen Binciken NSCDC, Sun Bude wa Jami'ai Wuta
- Jami'an hukumar NSCDC sun tsallake rijiya da baya bayan wasu 'yan ta'adda sun kai musu hari a yankin Borgu da ke jihar Neja
- Maharan sun lalata motar jami'an sannan suka sace bindiga guda daya da sauran kayayyakin amfani kamar wayoyi da tufafi
- Shugaban hukumar NSCDC ya tura dakaru na musamman yankin domin tabbatar da tsaron jami'ai da mazauna yankin Borgu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Hukumar NSCDC ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kai hari kan shingen binciken jami’anta a kan titin Wawa-Babanla na Karamar Hukumar Borgu a jihar Niger.
Kwamandan NSCDC na jihar, Suberu Siyaka-Aniviye, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Minna, ranar Laraba, inda ya ce ba a rasa rai a harin ba.

Source: Twitter
'Yan bindiga sun farmaki jami'an NSCDC
Siyaka-Aniviye ya ce maharan, da suka zo da yawa, sun kai harin ne da tsakar dare, amma ba su samu damar yin abin da suka ga dama ba saboda ƙoƙarin jami’an da ke bakin aiki, in ji rahoton Channels TV.
A cewar sanarwar jami'in hulda da jama'a na rundunar, DSC Abubakasr Muti, lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:28 zuwa 1:00 na daren 22 ga Disamba, 2025.
Sanarwar ta ce wasu gungun 'yan bindiga da ba a san yawansu ba sun farmaki shingen binciken tare da bude wuta kan jami'an NSCDC da ke bakin aiki.
Siyaka-Aniviye ya ce jami’an NSCDC sun yi yunƙurin fatattakar maharan, amma lamarin ya yi ƙamari saboda yawan maharan da kuma duhun dare a yankin.
Jami'an NSCDC sun tsere a harin 'yan bindiga
Ya bayyana cewa maharan sun rika amfani da fitilun hannu wajen gano duk wanda ke motsi kafin su buɗe wuta, lamarin da ya tilasta jami’an tsaron yin dabarun kaucewa harbi tare da neman mafaka.
“Jami’anmu sun yi dabarun kaucewa tare da ɗaukar matakan kariya, amma maharan sun rika harbe-harbe ba kakkautawa saboda suna da makamai da yawa,” in ji kwamandan.
Siyaka-Aniviye ya ƙara da cewa jami’an sun bar motar aikin su yayin da suke neman tsira, amma maharan, suna zaton jami’an na cikin motar, suka bude wa matar wuta.
Ya ce motar ta cika da ramukan harsasai, gilashin gaba ya fashe, sannan dukkan tayoyinta hudu sun huje. Daga baya aka canja tayoyin, aka kuma dawo da motar zuwa hedikwatar NSCDC da ke Minna.

Source: Original
An tura karin jami'an NSCDC
Ya ƙara da cewa maharan sun kwace bindiga guda ɗaya yayin da jami'in da ke bindigar ke ƙoƙarin neman mafaka, a cewar rahoton Premium Times.
Ya jaddada cewa babu wani jami’i da aka kashe ko aka ji masa munanan raunuka, sai dai wasu sun samu ƙananan raunuka yayin da suke tserewa.
Kwamandan ya ce babban kwamandan NSCDC na ƙasa, Ahmed Audi, ya tura tawagar jami’ai na musamman nan take zuwa jihar Niger domin ƙarfafa tsaro.
Rahotanni sun nuna cewa akwai ƙungiyoyin 'yan ta'adda da dama a Niger, wasu daga cikinsu na da alaƙa da ƙungiyoyin Boko Haram da Al-Qaeda.
An cakawa jami'ar NSCDC wuka
A wani laabrin, mun ruwaito cewa, wasu bata-gari sun cakawa jami’ar NSCDC, Akpan Blessing wuka a gaban gidanta da ke Abuja, wanda ya yi silar mutuwarta.
Makusantan jami'ar sun ce an kai Blessing asibitoci daban daban amma ba a karɓe ta ba saboda babu rahoton ‘yan sanda, abin da ya sa ta zubar da jini har ta mutu.
Rahoto ya nuna cewa wasu asibitocin sun ki karɓarta duk da an nuna masu katin aikinta na hukumar NSCDC, yayin da rundunar ta yi shiru kan wannan lamarin.
Asali: Legit.ng


