Kashim Shettima Ya Dauki Zafi game da Harin Bam da Aka Kai Masallacin Juma'a
- Sanata Kashim Shettima ya nuna matukar bacin ransa kan harin bam da aka kai wani masallacim Juma'a a Maiduguri, jihar Borno
- Mataimakin shugaban kasar ya ce tuni Shugaba Tinubu ya ba da umarnin girke karin dakarun tsaro domin kare rayukan al'umma a yankin
- Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci irin wannan hari ba, yana mai tabbatar da cewa duk mai hannu zai dandana kudarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kakkausar suka da Allah-wadai kan harin bam da aka kai wani masallaci da ke kasuwar Gamboru a Maiduguri, Jihar Borno.
Shettima ya yi tir da harin na kunar bakin wake, wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane biyar tare da jikkata wasu da dama.

Source: Facebook
Shettima ya bayyana harin a matsayin mummunan ta’addanci da aka aikata kan bayin Allah da ba su ji ba kuma ba kuma ba su ga ni ba, kamar yadda Channels tv ta kawo.
Mataimakin shugaban kasa ya ce wannan mummunan ibtila'i, hari ne kai tsaye ga zaman lafiya da tsaron ƙasa baki ɗaya.
Wane mataki gwamnatin Tinubu ta dauka?
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha, ya fitar, Shettima ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin dakarun tsaro yankin domin farautar waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya na aiki kafada da kafada da gwamnatin Jihar Borno da hukumomin tsaro domin kare mutane da muhimman wurare a Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar.
“Gwamnatin Tarayya ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na rushe zaman lafiya da tsaron ƙasarmu ba.
"Jami’an tsaro suna aiki dare da rana domin ganin an cafke masu hannu a wannan mummunan laifi tare da gurfanar da su gaban doka,” in ji Shettima.
Shugaba Tinubu ya umarci jami'an tsaro
Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin ƙara tsaurara ayyukan tsaro nan take a Jihar Borno, biyo bayan harin, rahoton Vanguard.
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin Tinubu na da cikakken ƙudiri na tabbatar da tsaron ƙasa, bisa tanadin kundin tsarin mulki.
“Muna jajanta wa gwamnatin Borno, al’ummar jihar da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan harin.
"Gwamnatin Tarayya na da tabbacin cewa waɗanda suka aikata wannan ta’asa za su fuskanci hukuncin da doka ta tanada,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya ƙare da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ba wa hukumomin tsaro dukkan goyon baya da kayan aikin da suke buƙata domin murƙushe ta’addanci da duk wasu nau’o’in aikata laifuffuka a faɗin ƙasar.
Pantami ya jajanta harin masallacin Borno
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami ya yi Allah wadai da harin bam da aka kai wani masallacin Juma'a a Maidugurin jihar Borno.
Pantami ya bayyana cewa ya samu labarin lamarin cikin tsananin baƙin ciki, inda harin ya faru ne a yammacin ranar Talata, 24 ga Disamba, 2025.
Farfesa Pantami ya roƙi Allah Ya tona asirin masu aikata wannan ta’asa, Ya hukunta su, tare da kawo dorewar zaman lafiya a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng


