Yajin Aiki zai Kare: ASUU Ta Cimma Yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya
- Kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya sun cimma matsaya kan sabunta yarjejeniyar shekarar 2009 bayan dogon tattaunawa da ta dauki lokaci
- Rahoto ya ce sabuwar yarjejeniyar ta tanadi karin albashi ga malamai, inganta tsarin fansho da sabon tsarin tallafin jami’o’in gwamnati
- An tsara fara aiwatar da yarjejeniyar ne daga 1, Janairu, 2026, tare da bukatar ASUU ga gwamnati ta cika dukkan alkawuran da aka dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa, ASUU, ta sanar da kammala tattaunawar sabunta yarjejeniyar shekarar 2009 da Gwamnatin Tarayya, yarjejeniya da ta dade tana janyo ce-ce-ku-ce a fannin ilimin jami’a a Najeriya.
ASUU ta ce sabuwar yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga 1, Janairu, 2026, kuma an tsara duba ta a duk bayan shekaru uku domin tabbatar da ci gaba da dacewarta da halin da ake ciki.

Source: Twitter
Sanarwar ta fito ne ta shafin Facebook na ASUU, inda ta bayyana cewa an cimma matsaya ne a ranar 23, Disamba, 2025, bayan shafe lokaci ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
Bukatun ASUU ta aka yarda da su
Sabunta yarjejeniyar ta mayar da hankali sosai kan walwalar malaman jami’o’i, inda aka amince da karin albashi kashi 40 cikin 100 ga dukkan ma’aikata masu koyarwa.
Wannan karin, a cewar ASUU, na da nufin rage matsin rayuwa da kuma dawo da martabar aikin koyarwa a jami’o’in gwamnati.
Baya ga karin albashi, yarjejeniyar ta tanadi ingantaccen tsarin fansho, musamman ga Furofesoshin da suka yi ritaya.
A karkashin sababbin sharudan, Furofesoshi za su rika karbar fansho da ya yi daidai da albashinsu na shekara guda bayan sun yi ritaya a shekaru 70, abin da ASUU ta bayyana a matsayin babban sauyi a tsarin kula da tsofaffin malamai.
Sabon tsarin tallafin jami’o’in Najeriya
Yarjejeniyar ta kuma gabatar da sabon tsarin tallafin kudi ga jami’o’in gwamnati, inda aka ware kasafi na musamman domin bincike, dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje, kayan aiki da kuma ci gaban ma’aikata.
Daily Trust ta rahoto cewa ASUU ta ce tsarin zai taimaka wajen inganta ingancin koyarwa da bincike a jami’o’in kasar.
Har ila yau, an gabatar da shawarar kafa majalisar bincike ta kasa wadda za ta tallafawa bincike, tare da tanadin a ware akalla kashi 1 cikin 100 na GDP na Najeriya domin wannan manufa.
‘Yancin jami’a da kariya ga ASUU
Daya daga cikin muhimman bangarorin yarjejeniyar shi ne karfafa ‘yancin jami’a da ‘yancin ilimi, tare da tabbatar da sabon tsarin zaben shugabannin a makarantu.

Source: UGC
Yarjejeniyar ta kuma bayar da tabbacin cewa babu wani da za a tsananta masa ko a hukunta shi saboda shiga gwagwarmayar yajin aiki.
A karshe, ASUU ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da gaggauta aiwatar da yarjejeniyar, tare da fadada tattaunawa da sauran kungiyoyin jami’a domin samar da kwanciyar hankali da dorewar tsarin ilimin jami’a a Najeriya.
Tinubu ya sauya sunan jami'o'i
A wani labarin, kun ji cewa tun zuwan shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan wasu manyan jami'o'i a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
An ware Musulmi a gefe da Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar $2bn da Amurka
A karon farko, Bola Tinubu ya sauya sunan jami'ar Abuja zuwa sunan tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon mai ritaya.
Haka zalika, shugaban ya sanyawa jami'o'i sunan Yusuf Maitama Sule, Muhammadu Buharu da Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Asali: Legit.ng

