Abin da Gwamna Abba Ya Ce bayan Samun Labarin Rasuwar 'Yan Majalisa 2 a Kano

Abin da Gwamna Abba Ya Ce bayan Samun Labarin Rasuwar 'Yan Majalisa 2 a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa rasuwar 'yan Majalisar dokokin Kano guda biyu ta jefa shi cikin yanayin kaduwa
  • A wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, Gwamna Abba ya mika sakon ta'aziyya ga majalisar dokokin Kano da al'ummar Ungoggo da Kano Municipal
  • Ya ce wannan rasuwa ta jajirtattun mutane masu kaunar jama'a jarabawa ce mai radadi, inda ya bukaci al'ummar Kano su zama masu hakuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matuƙar alhini da kaɗuwa kan rasuwar mambobi biyu na Majalisar Dokokin Jihar Kano a rana guda.

Yan Majalisar dokokin Kano da Allah ya yi wa rasuwa a jiya Laraba su ne Hon. Sarki Aliyu Daneji, mai wakiltar Kano Municipal da Hon. Aminu Sa’adu, wakilin Ƙaramar Hukumar Ungoggo kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya yi alhinin rasuwar 'yan majalisar dokoki 2 a jihar Kano

Gwamna Abba Kabir.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamma Abba ya bayyana matukar alhini a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Rasuwar 'yan majalisa 2 ta taba Gwamna Abba

Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwar 'yan majalisun biyu rana guda a matsayin wani mummunan al’amari mai raɗaɗi a tarihin Jihar Kano.

Ya ce wannan jarabawa ta jefa gwamnati da al’ummar Kano cikin alhini, inda ya jaddada cewa rasa ‘yan majalisa biyu masu ƙwazo cikin ‘yan awanni abu ne mai tayar da hankali da kalmomi kaɗai ba za su iya misaltawa ba.

A cewarsa, mamatan sun kasance jajirtattu, amintattun ‘yan siyasa, kuma ginshiƙai ga jama'arsu, domin jajircewarsu wajen aikin dokoki da hidimar al’umma ta wuce a misalta.

Gwamna Abba ya ce Jihar Kano ta yi babban rashi, domin ta rasa ‘ya’yanta biyu da suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jama’a hidima.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: 'Yan majalisar dokoki 2 sun mutu kusan lokaci guda a jihar Kano

Ya ƙara da cewa rasuwarsu ta bar giɓi mai girma a Majalisar Dokoki da kuma al’ummomin da suke wakilta.

Gwamna Abba ya mika sakon ta'aziyya

Ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, shugabanni da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano, da kuma al’ummar Ƙananan Hukumomin Kano Municipal da Ungoggo.

Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) da Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya lullube su da rahamarsa, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansu da al’ummar Kano hakurin jure wannan babban rashi.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Kano da su kasance masu haƙuri, haɗin kai da yawaita addu’a, yana mai bayyana wannan lamari a matsayin jarrabawa ga imani.

Yan majalisar Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf da yan majalisa 2 da Allah ya karbi rayuansu a Kano Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

An riga an yi jana’izar marigayi Hon. Aminu Sa’adu a makabartar Ungoggo, yayin da jana’izar marigayi Hon. Sarki Aliyu Daneji za ta gudana da ƙarfe 10:00 na safiyar Alhamis a masallacin fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Gwamna Abba ya ce:

“A madadin gwamnati da al’ummar Kano, muna miƙa sakon ta’aziyya ga Majalisar Dokoki ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Jibrin Ismail Falgore, da kuma iyalan mamatan, Allah Ya sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarsu ta ƙarshe. Amin.”

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kalaman Kwankwaso kan masarautar Kano sun tayar da kura

Sanata Barau ya mika sakon ta'aziyya

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Barau I. Jibrin ya yi matukar jimami tare da mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan ya kuma yi addu'ar Allah Ya gafarta wa mamatan, ya kuma sanya su a cikin gidan Aljannah.

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa wannan babban rashi ne mai radadi, tare da rokon Allah Ya ba iyalan mamatan hakuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262