Sheikh Ahmad Gumi Ya Maka Wasu Mutum 2 a Kotu kan Rubutun da Suka Yi a Facebook
- Babban malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya kai karar wasu mutum biyu gaban kotu
- Dr. Ahmad Gumi ya kai karar mutanen kotu ne bisa wani rubutu da suka yi a dandalin Facebook, kuma suka jingina masa
- Lauyan Sheikh Gumi, Suleiman Lere, ya ce ya kamata wannan shari’ar ta zama darasi ga masu amfani da kafafen sada zumunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shigar da ƙara gaban Kotun Majistare da ke Jihar Kaduna a kan wasu masu amfani da Facebook.
Sheikh Ahmad Gumi ya kai karar mutanen biyu ne bisa zargin haɗin baki wajen aikata laifi da wallafa rubuce-rubucen ɓatanci da aka jingina masa ƙarya.

Source: Facebook
Sunayen wadanda Ahmad Gumi ya kai kara
Premium Times ta ce karar, mai lamba KMD/685/25, wadda aka shigar a ranar Laraba, ta bayyana George Udom da Bello Isiaka a matsayin waɗanda ake ƙara, yayin da Sheikh Gumi shi ne mai ƙara.
A cewar takardun kotu, ana zargin waɗanda ake ƙarar da wallafa wani saƙo a Facebook a ranar 23 ga Disamba, 2025, inda suka jingina wa Sheikh Gumi wasu maganganu.
Ana tuhumar mutanen biyu da kirkirar karya tare da jinginawa Shekh Gumi, inda suka yi ikirarin shi ya fadi kalaman ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa.
Wane laifi ake zargin sun aikata a Facebook?
Saƙon da wadanda ake zargin suka wallafa, suka yi ikirarin Sheikh Ahmad Gumi ne ya fada, shi ne:
“Idan Ministan Tsaro Christopher Musa bai dakatar da hare-haren sojoji kan ’yan bindiga ba, za a hallaka dukkan iyalinsa da ke Zango Kataf a Kudancin Kaduna.”
A cikin ƙarar da ya shigar, Sheikh Gumi ya ce rubutun ya nuna tamkar shi ne ya yi barazana ga wani babban jami’in gwamnati da kundin tsarin mulki ya ɗora masa alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
Sheikh Gumi ya musanta fadar kalaman
Ta bakin lauyansa, Suleiman Lere, Sheikh Gumi ya musanta rubutawa ko amincewa da wannan saƙo, inda ya bayyana shi a matsayin “ƙage, rashin hankali da aka tsara shi da gangan.”
Ya ce wallafar ta yi mummunar illa ga mutuncinsa a matsayin malami da aka sani da wa’azin zaman lafiya, tattaunawa da kauce wa tashin hankali, tare da jefa shi cikin barazana.
Babban malamin ya kuma bayyana cewa jingina masa kalaman na iya jefa rayuwarsa cikin haɗari, domin irin waɗannan zarge-zarge na iya haddasa kai masa hari ko kuma janyo masa matakan da ba su dace ba daga hukumomin gwamnati.

Source: Facebook
Da yake magana kan shari’ar, lauyan Sheikh Gumi, Suleiman Lere, ya ce shari’ar ya kamata ta zama darasi ga masu amfani da kafafen sada zumunta da ke yaɗa ƙarya da ɓatanci.
Ya ce:
“Lokacin da mutane ke ɓoye kansu ta wayar hannu domin lalata mutuncin wasu ya wuce.”
Wani mai amfani da Facebook kuma mai bibiyar Sheikh Ahmad Gumi ya ce irin wannan matakin ya kamata malamai da yan siyasa su rika dauka kan masu bata masu suna.
Matashin mai suna, Mu'azu Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa galibin masu cin mutuncin malamai a soshiyal midiya ba su san hukuncin da zai iya hawa kansu ba idan aka kai su kara.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura tawaga Morocco yayin da Najeriya za ta fafata da Tanzania a AFCON 2025
"Malam ya mun daidai wallahi, saboda matasan mu, musamman a nan Arewa ba su san dokar amfani da kafafen sada zumunta ba, hukunta masu cin mutunci da kage zai iya zama darasi ga saura," in ji shi.
Sakon Sheikh Gumi ga Ministan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa ba ya goyon bayan duk wani tsari da zai bai wa ’yan bindiga damar ci gaba da aikata ta’addanci.
Sheikh Gumi ya yi tsokaci kan kalaman sabon ministan tsaron Najeriya, Janar CG Musa (mai ritaya), wanda ya ce babu sasanci da ’yan bindiga.
Malamin ya bayyana cewa wannan matsaya ta yi daidai da tsarin da ya dace da aikin soja, domin ya nuna ƙarfin gwamnati da ƙudirinta na kawo ƙarshen ta’addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

