Kwana Ya Kare: 'Yan Majalisar Dokoki 2 Sun Mutu kusan Lokaci Guda a Jihar Kano
- An tabbatar da rasuwar mambobi biyu na Majalisar dokokin jihar Kano cikin awa guda yau Laraba, 24 ga watan Disamban 2025
- Yan majalisar da Allah ya yi wa rasuwa su ne Hon. Aminu Sa’ad Ungogo, mai wakiltar mazabar Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji na Kano Municipal
- Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ya tabbatar da rasuwar 'yan majalisar amma bai yi cikakken bayani ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar Dokokin Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta rasa biyu daga cikin mambobinta kusan lokaci guda a yau Laraba, 24 ga watan Disamba, 2025.
Bayanai sun nuna cewa Hon. Aminu Sa’ad Ungogo, wanda ke wakiltar mazabar Ungogo a Majalisar Dokokin jihar Kano ya riga mu gidan gaskiya.

Source: Twitter
'Yan majalisa 2 sun rasu cikin sa'a 1 a Kano
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bayan haka kuma an tabbatar da rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji, wanda yake wakiltar mazabar Kano Municipal kuma dukansu sun rasu ne a yau Laraba.
An sanar da rasuwar Hon. Aminu Sa’ad Ungogo ne ta hannun Mai Ba Gwamna Abba Kabir Yusuf Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Ibrahim Adam.
A wata sanarwa da ya fitar, hadimin gwamnan ya ce:
“Allah Ya gafarta wa Hon. Aminu Sa’ad Ungogo, dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazabar Ungogo.”
Kusan awa guda bayan haka, aka kuma tabbatar da rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji ta hannun kakakin Gwamna Abba na jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Kakakin gwamnan Kano ya sanar da rasuwar
A wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai magana da yawun gwamnan Kano ya ce:
"InnalilLahi wa Inna ilaihi raji'un. Hon. Aminu Saad Ungoggo, 'dan Majalisar dokokin Kano mai wakiltar mazabar Ungoggo ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya. Ya rasu a yau kuma za a yi jana'izarsa da yamma a mahaifarsa Ungoggo, Kano."

Kara karanta wannan
Kano: Barau ya zargi Abba da take hakkin Alfindiki, ya ba shi kudin da aka hana shi
Mintuna kadan bayan haka, Sanusi Bature ya tabbatar da rasuwar 'dan majalisar Kano Municipal, Hon. Sarki Aliyu Daneji, inda ya ce:
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji’un. Hon. Sarki Aliyu Daneji, dan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazabar Kano Municipal, ya rasu a yau awa guda bayan rasuwar abokin aikinsa.”

Source: Facebook
Har yanzu babu wani cikakken bayani a hukumance daga gwamnatin jihar Kano ko majalisar dokoki kan abubuwan da suka yi ajalin 'yan majalisar guda biyu a cikin awa guda.
Sanata Isa Obaro ya kwanta dama
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon 'dan Majalisar dattawa, Sanata Isa Abonyi Obaro, wanda da ya wakilci mazabar Okehi/Okene a tsohuwar jihar Kwara, ya riga mu gidan gaskiya.
Majiyoyin sun ce marigayin ya bayar da gudummawa a kan dokoki da manufofin da suka shafi ci gaban mazabarsa da walwalar al’ummar yankin.
Sanata Natasha Akpoti ta tura sakon ta'aziyya ga al'ummar mazabarta watau Kogi ta Tsakiya bisa rasuwar sanatan wanda ya wakilci mazabar Okene/Okehi a tsohuwar jihar Kwara.
Asali: Legit.ng
