Sanata Ndume na Neman Dawo da Hannun Agogo baya game da Sababbin Dokokin Haraji

Sanata Ndume na Neman Dawo da Hannun Agogo baya game da Sababbin Dokokin Haraji

  • Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da aiwatar da sababbin dokokokin haraji saboda zarge-zargen da suka taso
  • Majalisar wakilai ta nuna damuwa kan yadda abin da aka sanya wa hannu ya bambanta da na jikin takardun dokokin da gwamnati ta fitar
  • Ndume ya ce dole a kafa kwamiti na musamman don tabbatar da gaskiyar zarge-zargen kafin ranar 1 ga watan Janairun 2026 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa kuma sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu game da sababbin dokokin haraji.

Sanata Ali Ndume ya bukaci shugaban kasa da ya dakatar da aiwatar da sababbin dokokin haraji da aka tsara za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan

Atiku da NBA sun fadi hadarin da suka gani a dokar harajin Tinubu ta 2026

Sanata Ali Ndume ya yi magana game da zargin samun jabun takardun dokokin haraji.
Sanata Ali Ndume ya na magana a zauren majalisar dattawa da ke Abuja. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Facebook

Bambanci a bayanan dokokin haraji

Wannan kira na Ndume ya biyo bayan zarge-zargen buga takardun jabu na dokokin harajin, inda ake ikirarin cewa bayanan da aka gani a takardun da aka buga sun bambanta da wadanda majalisun dokokin tarayya suka amince da su, in ji rahoton The Cable.

A ranar 17 ga Disamba, Abdussamad Dasuki, wani mamba a majalisar wakilai daga jihar Soko, ya bayyana cewa dokokin harajin da aka buga a jaridar gwamnati sun sha bamban da wadanda majalisa ta amince da shi.

Sakamakon haka, majalisar wakilai ta kafa kwamiti mai mambobi bakwai don bincikar wadannan bambance-bambance da aka samu a cikin takardun dokokin harajin.

Jabun dokar haraji: Sakon Ndume ga Tinubu

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Sanata Ndume ya bukaci Tinubu da ya kafa wani kwamiti na musamman don gano gaskiyar zargin canza fasalin dokokin harajin.

Ya jaddada cewa ci gaba da aiwatar da dokokin harajin ba tare da warware wadannan zarge-zarge ba zai haifar da kalubale ga sahihancin dokokin harajin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: An hango jirgin leken asirin Amurka yana shawagi a Najeriya

Ndume ya ce idan har zargin canza bayanai ya zama gaskiya, to dokar ba za ta taba zama halastacciya ba domin ba za a iya gina wani abu a kan rashin gaskiya ba.

Majalisar wakilai ta nuna damuwa game da bambancin da aka samu a takardun haraji da ta sanya wa hannu da wanda gwamnati ta buga.
Abbas Tajudeen yana jagorantar zaman majalisar wakilai, inda aka gano kuskure a takardun haraji. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Lauyoyi sun bukaci a dakatar da dokokin

Ba iya Sanata Ndume ba, ita ma kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta bukaci a dakatar da aiwatar da dokar a ranar Talata, tana mai cewa dambarwar da ta dabaibaye dokokin harajin na haifar da shaku kan gaskiya da martabar tsarin yin doka a Najeriya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin NBA na X, shugaban kungiyar, Mazi Afam Osigwe, SAN ya ce:

"A dakatar da aiwatar da sababbin dokokin haraji har zuwa lokacin da za a warware dukkan zarge-zargen da ke tattare da wadannan dokoki."

A bangarensa, Sanata Ndume ya kuma ce akwai bukatar shugaban kasa ya saurari kiraye kirayen kungiyoyin farar hula da al'ummar Arewa na ya janye dokar tare da bincikar zargin da ake yi.

Matasa sun yi wa dokokin haraji zanga zanga

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu matasan Najeriya sun fito zanga-zangar adawa da dokokin harajin Bola Tinubu da suka ce an sauya su a kwanan nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sa lokacin da sababbin jakadu za su fara aiki bayan amincewar majalisa

Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa sababbin tanade-tanaden dokokin sun tauye hakkokin jama’a tare da bai wa jami’an haraji iko fiye da kima.

Kungiyar matasan jam'iyyar ADC ta bukaci dakatar da aiwatar da dokokin da ake shirin yi a farkon 2026 tare da neman mayar da su majalisa domin gyara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com