An Yi Babban Rashi: Tsohon Wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Ya Rasu

An Yi Babban Rashi: Tsohon Wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya Ya Rasu

  • Rahotanni sun nuna cewa Allah ya karbi ran tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Cif Christopher Mbanefo yana da shekaru 95
  • 'Dansa, Victor Mbanefo ya tabbatar da labarin rasuwar Mbanefo amma bai bayyana cuta ko rashin lafiyar da ta zama ajalin marigayin ba
  • An bayyana marigayi Mbanefo a matsayin mutum mai taimakon jama’a, musamman a fannin ilimi, inda ya ba da gudummuwa sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - Fitaccen ɗan diflomasiyyar Najeriya da ya wakilci kasar a Majalisar Dinkin Duniya (UN), Cif Christopher Mbanefo, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Mbanefo, wanda ƙwararren akawu ne kuma masani a fannin ilimi, ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

Christopher Mbanefo.
Tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Cif Christopher Mbanefo Hoto: Angela James Amakaeze
Source: Facebook

An tabbatar da rasuwar Christopher Mbanefo

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa dansa, Victor Mbanefo, ya tabbatar da rasuwar mahaifinsu a wata sanarwa da ya rattaba wa hannu.

Kara karanta wannan

"Zan doke Gwamna Alia," An samu wani farfesa da zai shiga takarar gwamnan Benue

Ya ce:

“Cikin baƙin ciki da godiya, mu na sanar da rasuwar ubangidanmu, Cif Arthur Christopher Izuegbunam Mbanefo, Odu III na Onitsha, wanda Allah ya karɓi rayuwarsa a wannan wata na Disamba.

Ya ƙara da cewa iyalai za su sanar da tsarin jana’iza nan ba da jimawa ba, amma dai bai bayyana takamaiman lokaci da wurin da Mbanefo ya rasu ba.

Haka zalika, sanarwar ba ta bayyana hakikanin cuta ko rashin lafiyar da ta zama ajalin tsohon wakilin Najeriya a Majalisar dinkin suniya ba.

Taƙaitaccen tarihin marigayin

An haifi Christopher Mbanefo ne a ranar 11 ga Yuni, 1930, kuma ya fito daga Onitsha, a Ƙaramar Hukumar Onitsha ta Arewa, Jihar Anambra.

Marigayin ya taɓa zama wakilin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), sannan ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami’ar Lagos (UNILAG), Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), da Jami’ar Ahmadu Bello (ABU).

An naɗa shi wakilin Najeriya a UN a shekarar 1999 ta hannun tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Christopher Mbanefo.
Tsohon jami'in diflomasiyyar Najeriya,Christopher Mbanefo Hoto: Christopher Mbanefo
Source: Facebook

An bayyana marigayi Mbanefo a matsayin mutum mai taimakon jama’a, musamman a fannin ilimi, inda ya kafa cibiyar Arthur Mbanefo Digital Research Center a Jami’ar Lagos.

Tarihin karatun Cif Mbanefo

Marigayin ya yi karatun firamare da sakandare a Saint Patrick’s College da ke Kalaba a Kuros Riba, sannan ya tafi Birtaniya, inda ya zama Akanta a tsakiyar shekarun 1950.

Ya kasance mamba kuma shugaba na cibiyar kwararrun Akantoci Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN), tare da zama mamba na kungiyar ta reshen Ingila.

Tsohon Sanata daga Delta ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Sanatan da ya wakilci Delta ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya, Peter Nwaoboshi ya riga mu gidan gaskiya.

Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori , ya nuna alhini matuƙa, yana cewa rasuwar Nwaoboshi babban rashi ne ga Delta, Anioma da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya tuna rawar da Nwaoboshi ya taka a Majalisar Dattawa, musamman a matsayin shugaban kwamitin harkokin Niger Delta, inda ya nuna ƙwazo da jajircewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262