Kwara: Babban Sarki da Ƴan Bindiga Suka Sace Ya Tsira bayan Shafe Kwana 25

Kwara: Babban Sarki da Ƴan Bindiga Suka Sace Ya Tsira bayan Shafe Kwana 25

  • Wani Basarake da yan bindiga suka sace a jihar Kwara ya shaki iskan yanci bayan shafe kusan wata daya ba a sanhalin da yake ciki ba
  • Bayagan Ile a Kwara, Ojibara Kamilu Salami, ya samu ‘yanci bayan biyan kudin fansar da ba a fayyace ba saboda dalilai na tsaro a yankin
  • Al’ummar garin sun tarbi basaraken da murna, bayan an biya kudin fansa mai yawa har kashi biyu, wanda jama’ar gari kadai suka tara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Ojibara na Bayagan Ile a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara ya shaki iskar yanci bayan garkuwa da shi.

Oba Kamilu Salami, wanda ‘yan bindiga suka sace kwanaki 25 da suka wuce, ya fito bayan biyan miliyoyi.

Sarki ya shaki iskar yanci daga yan bindiga
Sarki Kamilu Salami da sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Sarki ya kubuta daga hannun 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Tankar mai ta kutsa cikin ayarin motocin Shugaban Majalisa, Akpabio, an rasa rai

Punch ta gano cewa an sace basaraken ne a gonarsa, kuma an sake shi da daren ranar Talata 23 ga watan Disambar 2025 bayan shafe kwanaki a hannun ‘yan bindiga.

Zuwan basaraken ya jefa al’ummar garin cikin murna da farin ciki, inda jama’a suka cika fadar domin taya shi da iyalansa murnar dawowarsa lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun yi cincirindo a fada, suna neman ganin basaraken tare da taya shi murna kan tsira da rayuwarsa.

Mai magana da yawun al’umma, Ayinla Lawal, ya tabbatar da sakin basaraken a safiyar Laraba 24 ga watan Disambar 2025 a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, an saki basaraken ne bayan biyan kudin fansa mai yawa har kashi biyu, wanda ‘yan bindiga suka bukata kafin sakin sa.

Ayinla ya ce al’ummar gari ne kadai suka tara kudin fansar, inda ya bayyana cewa ba a samu wani taimako daga gwamnati ba.

Ya ce:

“Ina farin cikin sanar da ku cewa an saki basarakenmu. An sake shi da daren Talata bayan mun sha wahala sosai.
“Manyanmu sun roke mu kada mu bayyana adadin kudin, amma kudin ya yi yawa. Gwamnatin jiha da ta ƙananan hukumomi ba su taimaka ba.”

Kara karanta wannan

Bayanai na kara fitowa a kan yadda gwamnati ta ceto daliban Neja

Sarkin da yan bindiga suka sace ya shaki iskar yanci
Taswirar jihar Kwara da ke fama da matsalolin tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Matakan da aka dauka domin yakar 'yan bindiga

Ayinla ya gode wa Allah da kafofin watsa labarai, yana mai cewa basaraken ya dawo gida da ransa, abin da ya fi komai muhimmanci.

Ya tunatar da cewa makonni biyu da suka wuce, ‘yan bindiga sun karbi Naira miliyan 10 amma suka ki sakin basaraken, cewar Daily Post.

A cewarsa, bayan karbar kudin, ‘yan bindiga sun sake bukatar karin Naira miliyan 15, wanda jama’ar gari suka yi fama sosai wajen tarawa.

Ayinla ya bayyana cewa ya na da kwarin gwiwar cewa ‘yan bindiga ba za su sake kai hari garin ba saboda karin tsaro.

Ya ce an dauki karin ‘yan banga da mafarauta domin kare garin, tare da fatan mazauna da suka gudu za su dawo.

'Yan bindiga sun bukaci N150m kan basarake

A baya, an ji cewa 'yan bindigar da suka sace babban Sarki a Kwara sun kira iyalinsa da safe, suna neman miliyoyin kudin fansa kafin su sake shi.

Kara karanta wannan

'Shirya komai aka yi': An 'gano' yadda rashin tsaro ya fara a Najeriya

Basaraken ya bace ne a gonarsa, inda aka tsinci babur dinsa kawai, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.

Wani manomi daga wani kauye mai makwabtaka ya shaida cewa ya ga lokacin da ’yan bindigar suka yi awon gaba da Sarkin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.