Asiri Ya Tonu: An Gano Mutanen da 'Yan Bindiga ke Amfani da Su wajen Karbar Kudi a Najeriya

Asiri Ya Tonu: An Gano Mutanen da 'Yan Bindiga ke Amfani da Su wajen Karbar Kudi a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta gano yadda wasu 'yan ta'adda ke amfani da masu PoS wajen karbar kudin fansa daga hannun mutane a Najeriya
  • Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka ya ce hukumomin tsaro na aiki tukuru don dakile lamarin
  • Ya ce har yanzu kudin fansa ne babbar hanyar samun kudaden 'yan bindiga kuma gwamnati na iya bakin kokarinta wajen shawo kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ’yan ta’adda ke ƙirƙiro sabqbbin hanyoyon karbar kudi daga hannun mutane musamman idan sun yi garkuwa da wasu.

Gwamnatin ta bayyana cewa 'yan ta'adda na amfani da na’urorin cire kudi (PoS), domin guje wa bin diddigi yayin aikata munanan ayyukansu.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wurin wani taro a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a hedkwatar cibiyar da ke Abuj, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ke sauke shafukan sada zumuntan 'yan ta'adda

Yadda yan bindiga ke amfani da masu PoS

Janar Laka ya nuna damuwa cewa kuɗin fansa na ci gaba da zama babbar hanyar samun kuɗaɗen da ’yan ta’adda ke amfani da su, inda ake yawan amfani da masu PoS wajen tura kuɗin.

Ya ce a lokuta da dama, ana tura kuɗin fansa zuwa asusun masu PoS, waɗanda daga bisani ke fitar da kuɗin su mika wa masu garkuwa da mutane, lamarin da ke wahalar da gano asalin kuɗin.

“Za ka ga an tura kuɗi, amma idan an bincika asusun, sai a gano na wani mai PoS ne. Masu garkuwa sukan bayar da lambar PoS, a tura kuɗin, sannan su je su karɓa,” in ji shi.

Wane mataki gwamnatin tarayya ta dauka?

Ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun ƙara ƙaimi wajen bibiyar kuɗin fansa, kama masu hannu a ciki da kuma rushe hanyoyin tallafa wa ta’addanci, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Sai dai bai bayyana cikakkun bayanai ba saboda dalilan tsaro, amma ya tabbatar da cewa an kama mutane da dama tare da gurfanar da su kan laifuffukan biyan fansa da tallafa wa ta’addanci.

Kara karanta wannan

Tsagin NNPP na son jawo matsala bayan babban taron su Kwankwaso a Abuja

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinhbu da wani mai sana'ar PoS Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Janar Laka ya jaddada cewa dabarun ’yan ta’adda na ci gaba da sauyawa, ciki har da amfani da sunan bogi da asusun da ba a tantance ba, inda ya ce hukumomin tsaro na ci gaba da sabunta dabarunsu domin tinkarar waɗannan ƙalubale.

Najeriya na kokarin rufe shafukan 'yan ta'adda

A baya, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce tana aiki kafada da kafada da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano tare da goge asusun da ’yan ta’adda.

Gwamnatin ta ce ta gano cewa ’yan ta’adda sun dade suna amfani da dandali irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X wajen sanar da hare-harensu.

Ta ce hukumomin tsaro sun yi taruka da dama da shugabannin kafafen sada zumuntar domin magance wallafe-wallafe da asusun da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262