Atiku Ya Fallasa Shirin Shugaban Kasa Tinubu kan Kudin Kananan Hukumomi
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taso Bola Ahmed Tinubu a gaba kan batun 'yancin kananan hukumomi
- Atiku Abubakar ya yi zargin cewa akwai abin da shugaban kasar yake son cimmawa shi ya sa ya ki aiwatar da hukuncin Kotun Koli
- Ya ce shugaban kasar na nuna baki biyu kan batun 'yancin kananan hukumomi, abin da ya ke fadi da wanda yake aikatawa suka bambanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja -Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kin bin hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke.
Hukuncin na Kotun Koli ya umarci gwamnatin tarayya da ta fara ba kananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun rarraba kudi na tarayya (FAAC).

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 24 ga watan Disamban 2025.
Me Atiku ya ce kan Tinubu?
Atiku ya ce zuwa watan Yuli na shekara mai zuwa, gwamnatin Tinubu za ta shafe cikakkun shekaru biyu tana kin aiwatar da hukuncin Kotun Koli, yana mai bayyana hakan a matsayin kalubalantar doka kai tsaye, ba wai jinkiri kawai ba.
A cewarsa, ci gaba da rashin aiwatar da hukuncin wata dabara ce ta siyasa da aka tsara domin amfani da bin doka a matsayin makami na matsa wa gwamnonin adawa su koma jam’iyyar APC, tare da ci gaba da rike cikakken iko kan gwamnonin jam’iyya mai mulki.
"Wannan ba jinkiri ba ne. Kin bin doka ne kai tsaye. Kin ɗaukar mataki wata dabara ce ta siyasa, ana amfani da bin doka a matsayin kayan ciniki don amfanin jam’iyya.”
- Atiku Abubakar
Atiku ya ja kunnen Shugaba Tinubu
Jagoran adawar ya jaddada cewa hukuncin Kotun Ƙoli karshe ne kuma wajibi ne, ba zaɓi ba ne, yana mai gargaɗin cewa ci gaba da kin aiwatar da irin wannan hukunci na nufin karya kundin tsarin mulki da kuma saɓa wa rantsuwar da shugaban kasa ya yi.

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC
“Ta hanyar hana kananan hukumomi ’yancin kuɗinsu, ba gwamnonin jihohi kake ragewa karfi ba; al’umma ka ke azabtarwa, kuma kuna kara tsananta wahalar rayuwa a tsakanin jama'a."
- Atiku Abubakar
Ya kuma nuna abin da ya kira sabanin magana da aiki, inda ya ce duk da cewa gwamnati na bayyana goyon bayanta ga ’yancin kananan hukumomi, amma ta gaza aiwatar da hukuncin kotu da ya tabbatar da hakan.
Atiku ya ba Shugaba Tinubu mafita
Atiku ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya umarci Ministan shari'a ya aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli nan take, yana mai cewa wannan batu ba ya buƙatar barazana ko dabarun siyasa.

Source: Twitter
"Maganin matsalar yana da sauki, a umarci Ministan shari'a ya aiwatar da hukuncin nan take. Duk abin da ya gaza haka, gazawar shugabanci ce.”
- Atiku Abubakar
Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da yin shiru kan lamarin na aika sako cewa ikon siyasa da rinjayen jam’iyya sun fi muhimmanci a wurin gwamnati fiye da alhakin bin doka da jin daɗin ’yan Najeriya da ke fama da tsananin rayuwa.
“Najeriya na bukatar shugabanci da ke bin dokar da ya rantse zai kare, ba wanda ke karkatar da ita don ribar siyasa ba."
- Atiku Abubakar
Atiku ya yi wa matasa nasiha
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi muhimmin kira ga matasa.
Atiku Abubakar ya bukaci matasan da su tashi tsaye su shiga cikin harkokin gina kasa, don ka da su zama 'yan kallo.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci matasa su zama masu tsara makomarsu, tare da taka rawar gani wajen karɓar jagoranci daga tsofaffin shugabanni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

