Tsohon Minista: Abin da Ya Kawo Rikicin Aisha Buhari da Fadar Shugaban Ƙasa
- Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Simon Dalung, ya yi dogon bayani game da abin da ya fara kawo cikas a mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
- Dalung ya ce tsammani da kyakkywan zaton Buhari zai yaki cin hanci da rashawa a Najeriya ne ya sa jama'a suka zuba masa kuri'a don ya mulke su a 2015
- Ya yi ikirarin cewa amma a fitar farko, matar tsohon Shugaban Kasan ta dauko magana, ta yi abin da ya jawo cece-kuce da ya rikide zuwa samar da bangaranci a Aso Rock
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Simon Dalung, ya yi dogon bayani a inda ya yi bitar shugabancin marigayi tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa jama'ar Najeriya sun yi tururuwar zuba wa tsohon Shugaban Kasa kuri'a da zummar ya fitar da su daga halin da suke ciki.

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dalung ya ce zaben Buhari a watan Maris na 2015 ya kasance wani babban sauyi a tarihin dimokuradiyyar Najeriya.
Dalung ya magantu kan mulkin Buhari
Solomon Dalung ya kara da cewa ikirarin cewa Buhari ya dogara da gudunmawar talakawa wajen yakin neman zabe ya kara karfafa amincewar jama’a gare shi.
Sai dai, Dalung ya ce gwamnati ta fuskanci kalubalen zubewar kimarta tun da wuri bayan wani lamari da ya shafi agogon hannu da aka ce Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta sanya.
A cewarsa, duk da cewa wasu sun ce akwai nau’in agogon da ba na ainihi ba ne, lamarin ya jawo shakku a zukatan yan Najeriya musamman a kafafen sada zumunta.
Ya ce hakan ya jawo muhawara kan sabani game da yadda ake kallon rayuwar Buhari ta tsantseni mai sauki da yadda ake zargin rayuwar da iyalinsa ke rayuwa mai tsada.
'Agogon Aisha ya fusata Shugaba Muhammadu Buhari'
Dalung ya yi ikirarin cewa wannan lamari ya tayar da hankalin Fadar Shugaban Kasa, tare da kara tsananta rikicin samun kusanci da ikon gwamnati.
Ya ce Buhari, wanda karfinsa ya ta’allaka da amincin jama’a, ya dauki lamarin da muhimmanci fiye da yadda aka yi tsammani.

Source: Getty Images
Dalung ya kuma zargi wasu masu karfin fada a ji da ke kewaye da gwamnati da amfani da wannan yanayi wajen karbe iko da ware wasu daga harkar mulki.
A cewarsa, hakan ya sa aka rika keɓe Uwargidan Shugaban Kasa daga harkoki masu tasiri, inda aka maye gurbin da tsauraran matakan tsaro.
Ya karyata duk wani yunkuri na bata sunan Buhari bayan rasuwarsa, yana mai cewa tarihi ya kamata ya yi adalci kuma a karshe, Dalung ya yi addu’a ga marigayin yana cewa:
“Allah ya jikan babban Janar daga Daura.”
Ana zargin karbe madafun iko a hannun Buhari
A baya, mun wallafa cewa tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, ya yi zargin cewa mulkin marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya faɗa hannun wasu ’yan tsirarun masu fada a ji.

Kara karanta wannan
Musa Kamarawa ya yi rantsuwa da Alkur'ani kan zargin Matawalle game da ta'addanci
Dalung ya bayyana wannan ne a wani sako da ya fitar a yayin da ake cece-kuce game da abubuwan da da aka rubuta game da tsohon Shugaban a cikin littafin da ya jawo zazzafar muhawara.
A cewarsa, akwai wani shiri da aka tsara domin wanke Muhammadu Buhari a zukatan jama'a, sai dai ya ce shi kan shi Shugaban ya san an fi kwace iko da gwamnatinsa tun yana raye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

