Tashin Hankali: Tanka Makare da Fetur Ta Tarwatse a tsakiyar Gidan Mai a Bauchi
- Hankula sun tashi yayin da aka samu fashewar tankar dakon fetur a wani gidan mai lokacin da take kokarin sauke man da ta dauko
- Jami'an kashe gobara na Bauchi sun yi nasarar shawo kan gobarar kafin ta cinye daukacin gidan man, tare da fadin asarar da aka yi
- Kididdiga ta nuna cewa hadurran motocin mai na karuwa a Najeriya, inda aka samu mace-mace sama da 1,800 tun 2009 zuwa 2025
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Wata motar dakon man fetur ta fashe a yammacin ranar Litinin a gidan mai na Hamzat Ahmed Petroleum da ke garin Dass, hedkwatar ƙaramar hukumar Dass a jihar Bauchi.
Fashewar tankar man ya jawo lalacewar dukiyan miliyoyin Naira yayin da al'ummar da ke zaune a wurin suka shiga tsananin tashin hankali da gudun ceton rai.

Source: Facebook
Tankar fetur ta fashe a jihar Bauchi
Jaridar Leadership ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:20 na yamma yayin da motar shiga cikin gidan man, tana jiran lokacin da za ta juye man da ke cikinta.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa, kodayake ba a rasa rai ba a sanadiyyar fashewar, akwai fargabar cewa wasu mutane sun samu munanan raunuka a lokacin da hatsarin ya faru.
Ya bayyana cewa gobara ta tashi ne daga jikin motar da ta kwaso man kafin ta bazu zuwa sassan gidan man.
Jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Bauchi sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka samu nasarar shawo kan wutar kafin ta bazu zuwa daukacin gidan man.
Asarar da aka yi a gidan mai
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Bauchi, Dauda Pali, ya bayyana cewa an shawo kan wutar baki daya.
Pali ya ce har yanzu ba a gano takamaiman dalilin fashewar tankar man ba, amma an riga an fara bincike don gano abin da ya haddasa fashewar motar.
Ya kara da cewa gobarar ta lalata babura biyu, keke-napep daya, rumfar gidan man, da kuma injinan bayar da mai.

Source: Getty Images
Kididdigar hadurran motocin mai a Najeriya
Wannan ba shi ne karon farko da fashewar motar mai ke sanadiyyar mutuwar mutane da lalata kadarori da dama a Najeriya ba, ciki har da jihar Bauchi, in ji rahoton ICIR Nigeria.
A wasu lokuta, idan tankar mai ta fadi, mutane na garzayawa wuraren da irin wannan hatsari ya faru don dibar mai, wanda galibi ke karewa da gobara da mace-mace.
Bincike ya nuna cewa shekarar 2024 ita ce mafi muni a tarihi, inda fashewar tankar mai a Majia ta kashe mutane 181, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu a shekarar zuwa 266.
Rahoton Research Gate ya nuna cewa a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2025, Najeriya ta samu fashewar tankar mai akalla 172, wadanda suka haddasa mutuwar mutane 1,896.
Tankar fetur ta fashe a cikin mutane
A wani labari, mun ruwaito cewa, wata tanka makare da man fetur sama da lita 30,000 ta fashe a kan babban titin Abeokuta zuwa Sagamu a jihar Ogun.
Rahotanni sun bayyana cewa mummunar gobara ta tashi a tsakiyar jama'a da matafiya, wadanda ke zirga-zirga a kan babban titin kamar yadda aka saba.
Bayanai sun tabbatar da cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan mummunan hatsari, sai dai har yanzu ba a gama tantancin adadin wadanda suka mutu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


