ICPC Ta Jero Ma'aikatun da aka Fi Tsammanin Badakala a Najeriya a 2025

ICPC Ta Jero Ma'aikatun da aka Fi Tsammanin Badakala a Najeriya a 2025

  • Hukumar ICPC ta fitar da rahoto kan yin gaskiya da nagarta na 2025, inda ta ayyana wasu ma’aikatun gwamnati da ba su da maki ko daya a bana
  • Rahoton ya nuna cewa kamfanin NNPCL, Jami’ar Calabar na cikin ma'aikatun Najeriya da ba su samu ko maki daya ba a wannan shekarar
  • ICPC ta ce raunin tsare-tsaren cikin-gida da rashin bin doka na barazana ga amincewar jama’a da masu zuba jari a harkokin gwamnatin a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da cin-hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta bayyana wasu ma’aikatu, hukumomi da sassa na gwamnati a matsayin wuraren da ake tsammanin badakala a rahotonta na 2025.

Rahoton da aka fitar ya kunshi bayani bayan tantance ma’aikatu 357, inda aka duba tsarin kulawa, manufofin cikin-gida da bin ka’idoji da doka.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ke sauke shafukan sada zumuntan 'yan ta'adda

Ofishin hukumar ICPC
Hedkwatar hukumar ICPC a Abuja. Hoto: @icpcnigeria
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa ICPC ta ce ta yi amfani da jadawalin kimanta da'a da nagarta (EICS) tare da kididdigar ACTU domin auna yadda kowace hukuma ke tafiyar da al’amuranta.

Bayanin ICPC kan ma'aikatu a 2025

Rahoton ICPC ya nuna cewa hukumar kula da hakar man fetur ta kasa (NUPRC) ce ta zo ta farko da maki 91.83, sai hukumar inshora NDIC da maki 90.70, yayin da AMCON ta samu maki 89.93.

Sai dai rahoton ya jero NNPCL, Jami’ar Calabar, hukumar FCSC da cibiyar NCCSALW a cikin hukumomin da ba su samu ko maki daya ba.

Hukumar ta ce hakan ya nuna cewa kamfanin NNPCL, da wadanda ba su samu maki ba suna gaba-gaba a jerin ma'aikatun da za su iya fuskantar matsalolin badakala.

Wata ma'aikatar NNPCL a Najeriya
Wani sashe na ofishin kamfanin NNPCL. Hoto: NNPC Limited
Source: UGC

ICPC ta kuma bayyana cewa hukumomi 13 sun kasa mayar da martani gaba daya, lamarin da ya sa aka ware su a matsayin masu babban hadari.

Kara karanta wannan

An saka ranar da Trump zai hana 'yan Najeriya shiga kasar Amurka

Raunin tsare-tsare da matsalolin kudi

Rahoton ICPC ya nuna cewa ma’aikatu 102 ba su da tsare-tsaren dabarun aiki, yayin da 154 ba su da tsarin sa ido da tantance ayyuka.

Haka kuma, an gano cewa hukumomi 289 ba sa karfafa yin nazarin tsarin aiki ko tantance hadarin cin-hanci, yayin da 315 ba sa amfani da sakamakon irin wadannan bincike wajen yanke shawara.

Punch ta wallafa cewa a bangaren kula da kudi, rahoton ya ce hukumomi 99 ba su da ka’idojin ba da bashi ga ma’aikata, yayin da wasu ke ba da sababbin bashi ba tare da an biya tsofaffi ba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa wasu ma’aikatu ba sa mika rahotannin kudi ga ofishin babban akanta na tarayya, wasu kuma sun kasa mika kudin shiga kamar yadda doka ta tanada.

EFCC za ta gurfanar da kwamishina

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC za ta gurfanar da kwamishinan jihar Bauchi, Yakubu Adamu kan wasu zarge-zarge.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An fara neman a tsige Bola Tinubu daga kujerar shugaban kasa

A watannin da suka gabata hukumar ta kama kwamishinan bisa zargin karkatar da makudan kudi da suka kai N4.6bn.

Wasu bayanai sun nuna cewa za a gurfanar da shi ne tare da wani kamfani da ake zargin sun hada kai tare a badakalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng