Matasan ADC Sun Tsunduma Zanga Zanga kan Dokokin Harajin Tinubu
- Wasu matasan Najeriya sun fito zanga-zanga suna adawa da dokokin harajin Bola Tinubu da suka ce an sauya su bayan majalisar tarayya ta amince da su
- Masu zanga-zangar sun yi zargin cewa sababbin tanade-tanaden dokokin sun tauye hakkokin jama’a tare da bai wa jami’an haraji iko fiye da kima
- Kungiyar matasan jam'iyyar ADC ta bukaci dakatar da aiwatar da dokokin da ake shirin yi a farkon 2026 tare da neman mayar da su majalisa domin gyara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata zanga-zanga da matasan ADC suka shirya ta nuna adawa da dokokin haraji na shekarar 2026, wadanda suka ce an sauya su bayan majalisar tarayya ta kammala aikinta.
Shugaban matasan jam’iyyar ADC, na kasa, Balarabe Rufa’i, ne ya jagoranci zanga-zangar, inda ya ce matasan kasar nan sun fusata da yadda aka kakaba dokokin ba tare da sahalewar jama’a ba.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a X, Balarabe Rufa'i ya ce abin da ake zargin ya faru ya saba ka’idojin yin doka, tare da tauye gaskiya da amincewar jama’a kan dokokin da za su shafi rayuwarsu ta yau da kullum.
An yi zanga-zanga saboda dokokin haraji
Balarabe Rufa’i ya bayyana cewa dalilin zanga-zangar shi ne bambancin da ke tsakanin abin da majalisar tarayya ta tattauna da kuma abin da aka wallafa a hukumance bayan an amince da dokokin.
Ya ce sababbin tanade-tanaden da suka bayyana a cikin dokokin sun hada da tilasta biyan kashi 20 cikin 100 na kudin haraji kafin dan kasa ya iya kalubalantar tantancewar haraji.
A cewar shugaban matasan jam'iyyar ADC, wannan mataki zai sanya talakawa da dama cikin matsin lamba da wahala.
Haka kuma, ya ce an cire kulawar kotu wajen kwace kadarori, tare da bai wa jami’an haraji ikon kama mutane, lamarin da ya ce ya nuna karancin adalci da bin ka’ida.
Tasirin dokokin haraji kan ‘yan kasuwa
Rufa’i ya ce kananan ‘yan kasuwa, masu sana’o’i da masu dogaro da kananan ayyuka su ne ke fuskantar barazana mafi tsanani daga sababbin dokokin haraji.
A cewarsa, dokokin sun zo ne a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa, karancin ayyukan yi da tabarbarewar tattalin arziki, wanda hakan ke kara jefa ‘yan kasuwa cikin wahala.
Ya kara da cewa sauye-sauyen harajin VAT da aka gabatar na iya cutar da jihohin Arewa, ta hanyar karkatar da kudin shiga daga yankunan da tuni suke fuskantar rauni ta fuskar tattalin arziki.
Bukatun matasan ADC ga Bola Tinubu
Shugaban matasan ADC ya ce matasan Najeriya na bukatar daukar mataki cikin gaggawa domin magance wannan lamari.
Daga cikin bukatunsu akwai dakatar da aiwatar da dokokin haraji na 2026, tare da mayar da su majalisar gaba daya domin a sake duba su.
Sun kuma bukaci cire dukkan tanade-tanaden da suka bayyana a matsayin masu tsanani da hukunci, tare da tabbatar da rabon VAT cikin adalci da kare ikon tattalin arzikin kasa.

Source: Facebook
Rufa’i ya ce matasan ba sa adawa da biyan haraji gaba daya, sai dai suna bukatar dokoki da za su tallafa wa rayuwa da sana’o’in jama’a, ba dokokin da za su kara jefa mutane cikin talauci ba.
Atiku ya soki dokokin harajin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da dokokin harajin Bola Tinubu.
A sanarwar da ya fitar a cikin farkon makon nan, Atiku ya ce akwai bukatar gano gaskiya game da zargin sauya dokokin da aka ce an yi.
Kungiyar lauyoyi ta kasa, NBA ta bi sahun Atiku Abubakar wajen kira a dakatar da aiwatar da dokokin sai bayan cikakken bincke.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


