Kwankwaso Ya Fadawa Tinubu Tsarin da zai Yi kan Tsaro idan Ya Samu Mulkin Najeriya
- Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya daura masa wajen yaki da rashin tsaro
- Ya ce matsalar tsaro na kara ta’azzara ne sakamakon rashin cikakken kokari daga bangaren gwamnatin tarayya a yaki da ta'addanci a Najeriya
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin sauya tsarin tsaro idan ya samu damar jagorantar Najeriya a matsayin shugaban kasa a nan gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dauki matakin gaggawa kan matsalar rashin tsaro.
Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ya daurawa shugaban kasa alhakin zama babban kwamandan rundunar soji, don haka nauyin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa ya rataya a wuyansa.

Source: Twitter
Tribune ta rahoto cewa ya yi wannan jawabi ne yayin da yake magana da jama’a a Kano, inda ya zargi gwamnatin Tinubu da rashin nuna cikakkiyar niyya wajen tinkarar ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.
Kiran Kwankwaso ga Tinubu kan tsaro
Kwankwaso ya ce ana cigaba da kashe ‘yan Najeriya a wurare daban-daban, yayin da wadanda ke aikata laifukan ke tserewa ba tare da hukunci ba.
Tashar Arise News ta wallafa cewa ya ce wannan alama ce ta gazawar gwamnati wajen daukar matakin da ya dace domin kare rayuka.
Ya ce ya kamata Bola Tinubu ya tashi tsaye ya amsa sunan babban kwamandan sojoji, domin magance matsalolin tsaro da suka addabi al’umma.
A cewarsa, duk wata gwamnati da ta kasa kare rayuka da dukiyoyin jama’a ta gaza a aikinta, kuma ba ta da hujjar ci gaba da rike madafun iko.
Kwankwaso ya yabi sojojin Najeriya
Kwankwaso, wanda ya taba rike mukamin ministan tsaro, ya ce rundunar sojin Najeriya na daga cikin jarumai a duniya.
Tsohon gwamnan ya tunatar da rawar da sojojin kasar suka taka a ayyukan tabbatar da zaman lafiya a kasashen waje kamar Darfur da Liberia.
Ya ce ba su da kokonto kan kwarewa da jarumtar da sojojin Najeriya ke da shi, amma abin da ke hana samun nasara shi ne rashin isasshen goyon baya daga bangaren gwamnati.

Source: Facebook
Kwankwaso ya ce a lokacin da yake Ministan tsaro, ya san irin karfin da rundunar ke da shi, yana mai cewa idan aka basu kayan aiki da cikakken goyon baya, za su iya shawo kan matsalolin tsaro.
Kwankwaso zai dauki sojoji miliyan 1
Dangane da zaben 2027, Kwankwaso ya ce idan Allah ya ba shi damar zama shugaban kasa, zai sanya tsaro a sahun gaba na manufofinsa.
Tsohon Sanatan na yankin Kano ta tsakiya ya bayyana shirin daukar sama da sojoji miliyan 1 domin karfafa rundunar tsaron kasa.
Haka kuma, gawurtaccen 'dan siyasar ya ce zai hada kungiyoyin tsaron cikin gida da ake da su a jihohi cikin tsarin tsaron kasa.
Maganar Kwankwaso kan Aminu Ado Bayero
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan zaman da mai martaba Aminu Ado Bayero ke yi a fadar Nasarawa.
Kwankwaso ya bukaci 'yan sanda su dauki mataki a kan zaman da ya ke a fadar domin a cewarsa, shi ba halastaccen Sarki ba ne.
A daya bangare kuma, Kwankwaso ya yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa daukar 'yan sa-kai 2,000 domin karfafa tsaron jihar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


