Hadiman Gwamna Inuwa 4 Sun Shiga Matsala bayan Cin Zarafin Kansila a Gombe

Hadiman Gwamna Inuwa 4 Sun Shiga Matsala bayan Cin Zarafin Kansila a Gombe

  • Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sallami hadimai hudu nan take kan dukan kansilan Shamaki
  • Binciken kwamitin musamman da rahoton hukumomin tsaro ne suka tabbatar da laifin da suka aikata a jihar
  • Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci take doka ba, tare da tabbatar da zaman lafiya da adalci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da sallamar wasu hadiminsa guda hudu.

Matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar kan dukan da aka yi wa kansila Abdulrahman Abubakar Sheriff na mazabar Shamaki a karamar hukumar Gombe.

An sallami hadimai 4 a Gombe
Kansilan Shamaki, Abdulrahman Abubakar Sharif da Abdullahi Danko. Hoto: Adamu Danko.
Source: Facebook

Gwamnan jihar Gombe ya kori hadimansa 4

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na gwamnan, Isma’ila Uba Misilli, ya tabbatar a Facebook.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Gwamna ya yi nadamar marawa Tinubu baya a 2023

Misilli ya bayyana cewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya isar da wannan sako bayan kafa wani kwamitin musamman domin binciken lamarin.

Martanin APC, jama'a kan lamarin a Gombe

Tun da farko, jam’iyyar APC a Jihar Gombe ta yi kakkausar suka kan cin zarafin kansilan da wani hadimin gwamna ya yi, wanda aka dauka a bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Bidiyon ya nuna wani hadimin gwamna da ke karkashin Ofishin Shugaban Ma’aikata, mai suna Adamu Abdullahi Danko, yana dukan kansilan ba tare da ya iya kare kansa ba.

Kungiyoyin fararen hula da dama, ciki har da Amnesty International da Kungiyoyin Fararen Hula ta Jihar Gombe, sun yi Allah-wadai da dukan, tare da bukatar a hukunta wanda ya aikata laifin da kuma sallamarsa daga aiki.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da cewa yana nuna yadda take doka da danniya ke karuwa daga jami’an gwamnati.

Gwamna Inuwa ya kori hadimai 4 kan cin zarafin kansila
Gwamna Inuwa Yahaya, Kansilan Shamaki da tsohon hadiminsa, Adamu Danko. Hoto: Ismaila Uba Misilli, Adamu Danko.
Source: Facebook

Jerin hadiman gwamna da suka rasa kujerunsu

A cewar sanarwar Misilli, sakamakon binciken kwamitin ne ya sa gwamnan daukar wannan mataki.

Kara karanta wannan

APC ta fusata bayan hadimin gwamna ya lakadawa kansila dukan tsiya

Hadiman da abin ya shafa sun hada da Garba Mohammed Mai Rago hadimi a bangaren siyasa sai Rabiu Sulaiman Abubakar na bangaren kafafen sada zumunta da Ali Ibrahim Baban Kaya na bangaren hulda da al’umma.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayar da umarnin cewa sallamar ta fara aiki nan take, tare da bukatar hadiman da abin ya shafa su mika dukkan kayan gwamnati da ke hannunsu ga hukumomin da suka dace ba tare da bata lokaci ba.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Gombe cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da mutunta doka, gaskiya da zaman lafiya, yana mai jaddada cewa za a rika daukar matakai masu tsauri.

An yankewa basarake hukuncin kisa a Gombe

An ji cewa kotu ta kama basarake da wani mutum daya da laifin kisan kai a jihar Gombe inda ta yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Alkalin da ya jagoranci shari'ar, Abdulsalam Mohammad, ya wanke mutum uku da aka gurfanar da su tare saboda rashin hujjoji.

An dai kama tare da gurfanar da hakimin Bangunji, Sulei Yerima bisa jikkata wani mutumi, wanda raunin ya zama ajalinsa a Gombe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.