Atiku da NBA Sun Fadi Hadarin da Suka Gani a Dokar Harajin Tinubu ta 2026
- Kungiyar lauyoyi ta NBA da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun bayyana damuwa kan zargin sauya dokokin haraji bayan amincewar majalisa
- Rahotanni sun nuna cewa sun ce akwai barazana ga sahihanci da gaskiyar aikin majalisa, tare da kiran a dakatar da aiwatar da dokokin nan take
- Majalisar tarayya ta kafa kwamitin mutum bakwai domin binciken zargin, yayin da ake kara rade-radin matsin lamba kan bangaren zartarwa karkashin Bola Tinubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Lauyoyin Najeriya wato NBA tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun bukaci a dakatar da aiwatar da dokokin gyaran harajin Bola Tinubu.
Kungiyar NBA ta bayyana cewa ce-ce-ku-cen da ke tattare da dokokin na iya raunana amincewar jama’a ga tsarin dokokin kasa, tare da barazana ga gaskiya da rikon amana a majalisar dokoki.

Source: Getty Images
A sakon da ya wallafa a X, Atiku Abubakar ya bayyana zargin sauye-sauyen a matsayin hari ga ikon majalisa, yana mai cewa hakan na nuna rashin mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya.
Korafin NBA kan dokar harajin Tinubu
A wata sanarwa da shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya fitar, kungiyar ta ce dole ne a gudanar da bincike a bayyane kuma ba tare da boye-boye ba, domin fayyace yadda aka amince da dokokin harajin.
Shugaban NBA ya ce ya zama dole a dakatar da duk wani shiri na aiwatar da dokokin har sai an bincika kuma an warware dukkan wadannan zarge-zarge.
NBA ta kuma bayyana cewa rikicin da ke tasowa daga wannan ce-ce-ku-cen na iya girgiza yanayin kasuwanci, ya rage kwarin gwiwar masu zuba jari, tare da jefa ‘yan kasa da kamfanoni cikin rashin tabbas.
Atiku ya fadi hadarin sauya dokar haraji
Atiku Abubakar ya bayyana cewa zargin shigar da wasu ka’idoji ba tare da amincewar majalisa ba na nuni da akwai babbar matsala.
Ya ce ana zargin bangaren zartarwa da kara tilastawa jama'a da kakaba wa ‘yan kasa nauyi mai tsanani tare da cire hanyoyin sa ido kan jami'an haraji.
Ya kara da cewa wadannan sauye-sauyen sun mayar da jami’an haraji kamar jami’an tsaro, inda ake ba su ikon kama mutane, kwace kadarori, da sayar da su ba tare da umarnin kotu ba.
Atiku ya ce akwai kuma karin nauyin da aka kakaba wa ‘yan kasa, ciki har da wajabta ajiye kashi 20 cikin 100 na kudin haraji kafin daukaka kara, da tara mai yawa kan basussukan haraji.
Matsayar Atiku da NBA kan dokar haraji
Atiku da NBA sun bukaci Majalisar Tarayya da ta gyara duk wasu sauye-sauyen da ba bisa ka’ida ba, tare da hukunta duk wadanda aka samu da hannu.
Punch ta rahoto cewa sun kuma bukaci a dakatar da aiwatar da dokokin da aka shirya za su fara aiki a ranar 1, Janairu, 2026.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci bangaren shari’a da ya soke duk wasu sashe da suka sabawa kundin tsarin mulki, tare da kira ga EFCC da ta yi bincike tare da gurfanar da duk masu hannu a zargin.

Source: Facebook
A halin yanzu dai majalisar wakilai ta kafa kwamiti bincike da zai tattara bayanai game da zargin da aka yi kan dokar harajin Tinubu.
Sheikh Sani Jingir ya soki dokar haraji
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban majalisar malaman kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana kan dokar haraji.
Malamin ya yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake cikakken bincike game da korafe-korafen da jama'a ke yi a Najeriya.
A bayanin da ya yi, Sheikh Jingir ya ce bai kamata shugaban kasa ya daura wa jama'ar Najeriya abin da ya fi karfinsu ba da sunan haraji.
Asali: Legit.ng


