"Ba Gwamnoni ba Ne: Gwamna Radda Ya Fadi Mai Laifi kan Tsadar Rayuwa

"Ba Gwamnoni ba Ne: Gwamna Radda Ya Fadi Mai Laifi kan Tsadar Rayuwa

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna damuwa kan matsin lambar da ake yi wa gwamnoni a Najeriya
  • Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa bai kamata ana dorawa gwamnoni laifi ba duk lokacin da aka samu tsadar rayuwa
  • Gwamnan ya nuna cewa gwamnoni fa ba su ba ne ke samun kaso mai tsoka na kudaden da ake rabawa duk wata daga asusun tarayya

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci ’yan Najeriya da su daina ɗora wa gwamnonin jihohi laifin tabarbarewar tattalin arzikin kasa.

Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ce ke karɓar fiye da rabin kudaden shiga na tarayya da ake rarrabawa kowane wata.

Gwamna Radda ya kare gwamnoni
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a wata hirar da ya yi da tashar RFI Hausa wadda aka sanya a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

"Ba Gwamnoni ne kadai barayi a Najeriya ba": Dikko Radda ya dauki zafi

Gwamna Radda ya kare gwamnoni

A cewarsa, duk da cewa ana yawan karkatar da fushin jama’a kan karuwar tsadar rayuwa ga gwamnonin jihohi da shugabannin kananan hukumomi, amma a zahiri gwamnatin tarayya ce ke karɓar mafi yawan kudaden asusun tarayya.

"Duk lokacin da aka shiga tsadar rayuwa, mutane suna zargin gwamnonin jihohi da kananan hukumomi."
"Amma idan aka zo rabon kuɗaɗen shiga, kashi 52 cikin 100 na zuwa ga gwamnatin tarayya. Kashi 48 cikin 100 ne kawai ake rabawa jihohi 36 da kananan hukumomi 774.”

- Gwamna Dikko Radda Umaru Radda

Radda ya ce gwamnatin tarayya ke kwashe kudi

Gwamnan ya bayyana cewa tsarin rabon kudaden shiga na barin gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi cikin matsin lamba wajen biyan buƙatun jama’a da ke karuwa a kodayaushe.

Ya ce mutane da dama na da ra’ayin cewa gwamnonin jihohi ne ke karbar kaso mao rinjaye kan dukiyoyin ƙasa.

Da yake tambayar tasirin shekaru da dama na ikon gwamnatin tarayya kan kudaden shiga na kasa, Gwamna Radda ya ce ya dace ’yan Najeriya su duba yadda aka yi amfani da kudaden da aka tara a matakin tarayya tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Shan suka kan ziyarar Nnamdi Kanu ta sa gwamna ya fadi lokacin daina siyasa

"Tsawon shekaru da dama, gwamnatin tarayya ce ke karɓar mafi yawan kudaden tarayya. Don haka tambayar da ya kamata ’yan Najeriya su yi ita ce: ina yawancin waɗannan kuɗaɗen suka tafi?”

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Wannan jawabi na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara matsin lamba kan gwamnatocin jihohi da su yi bayani kan karin kudaden da suke samu bayan cire tallafin man fetur.

Gwamna Radda ya kare gwamnoni kan zarge-zarge
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Me Radda ya ce kan zargin cin hanci?

Gwamna Radda ya kuma yi watsi da zargin cin hanci da rashawa da ake yawan jingina wa gwamnonin jihohi, yana mai gargadin a guji yin kudin goro.

Ya ce ya dace a auna shugabanci bisa ɗaiɗaikun mutane, yana mai jaddada cewa ba dukkan shugabannin da aka zaɓa ba ne masu cin hanci da rashawa.

Radda ya kaddamar da aiki kan lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki.

Gwamna Radda ya kaddamar da aikin gina tashar wutar lantarki ta ruwa mai ƙarfin megawatt 1 (1MW) a karamar hukumar Danja.

Ana sa ran aikin zai samar da wutar lantarki mai tsafta, araha kuma abin dogaro ga al’ummomin kananan hukumomin Danja, Kafur da kewaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng