Gwamna Abba Ya Ja Tawaga, Ana Kaddamar da Sabuwar Hukumar Tsaro a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara kaddamar da hukumar tsaro ta jiha mai suna 'Kano State Neighbourhood Watch Corps' a filin wasa na Sani Abacha
- Gwamnati ta kaddamar da hukumar ne a yayin da Kano ta fara fama da barazanar 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane a wuraren da ke iya da Katsina
- Sanarwar da Mai Magana da yawun gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta cewa za a tura jami’ai 2,000 zuwa kananan hukumomi 44 domin yaki da manyan laifuka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya fara kaddamar da sabuwar rundunar tsaro mallakin jihar wato 'Kano State Neighbourhood Watch Corps'.
An fara bikin kaddamar da hukumar a wani taro na musamman na faretin kammala horo da aka gudanar a ranar Talata, 23 ga watan Disamba, 2025 a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisa, Bello El Rufai ya lale miliyoyi domin taimakon karatun mutane a Kaduna

Source: Facebook
Wata Sanarwa da Darekta Janar kan kafafen yada labaran gwamna, Sanusi Bature D-Tofa da aka fitar da saiya ta ce za a yaye jami'an domin inganta tsaron jiha.
An kaddamar da hukumar tsaro a Kano
Premier radio ta wallafa cewa jimillar jami’ai 2,000 aka dauka aiki a wannan sabon shiri, inda 1,870 maza da 130 mata za su rika aiki a karkashin rundunar.
Za a tura su zuwa dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano domin taimakawa hukumomin tsaro wajen yaki da manyan laifuffuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar za ta samu cikakken kayan aiki, ciki har da makamai da alburusai, domin ba su damar fuskantar barazanar tsaro yadda ya kamata.
Haka kuma, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai mika motoci 88 na Hilux da kuma babura 440 ga sabuwar rundunar domin saukaka ayyukansu a fadin jihar.
Gwamnan Katsina ya nemi hadin kai
A yayin da ake ci gaba da taron a Kano, Premier Radio Kano ta wallafa wani bidiyo da ke nuna Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, yana magana kan muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jihohi.

Source: Facebook
Gwamna Dikko Radda ya ce:
"Rashin tsaro ba ya la'akari da jiha. Dole ne dabarun tsaronmu su zama na bai daya a tsakanin jihohinmu. Ina bada da shawara mu gwamnonin Arewa maso Yamma mu yi aiki tare domin tabbatar da tsaro."
Ya kara da cewa:
"A shirye gwamnatin Katsina ta ke wajen aikin da ya kamata."
Gwamnan ya kuma nanata kudurin gwamnatinsa na aiki kafada da kafada da sauran jihohi domin inganta rayuwar ‘yan sa kai da ke taka rawa wajen kare lafiyar jama’a.
A halin da ake ciki, ana ci gaba da taron kaddamarwar a Kano, inda ake jiran sauran manyan baki su gabatar da jawabansu daya bayan daya.
Daga cikin manyan baki da suka halarta akwai Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Gwamna Dikko Umaru Radda, da kuma wasu manyan jami’ai daga ciki da wajen Jihar Kano.
Kano: Yara sun kai karar mahaifinsu kotu

Kara karanta wannan
Abba Hikima, Ɗan Bello sun tsayawa ƴan N power a kotu, ana shirin ƙwato masu hakkinsu
A wani labarin, mun wallafa cewa fitaccen attajiri kuma dattijo a jihar Kano, Alhaji Isma’ila Mai Biskit, ya shiga wani hali na damuwa da ƙunci sakamakon rikicin cikin gida da ya ɓarke a tsakanin sa da wasu yaransa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ’ya’yan dattijon sun kai shi gaban kotu, suna zarginsa da cewa ba ya da cikakken ikon yanke shawara kan dukiyarsa, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin iyali
Ya ce Allah SWT ya jarrabe shi da rashin lafiya mai tsanani, wanda ya sa ya yanke shawarar tafiya Dubai domin neman magani. Saboda bukatar kudin jinya, ya sayar da wasu kadarorinsa, amma yaran su ka fusata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
