Sojoji Sun Cafke Ƴan Sanda kan Saɓa Umarnin Tinubu game da Gadin Ƴan Siyasa
- Rundunar sojoji ta cafke jami’an ‘yan sanda huɗu da ake zargi sun saba umarnin da Bola Tinubu ya bayar domin karfafa tsaro a Najeriya
- Rahotanni sun ce an kama jami’an ne a Abuja, yayin da suke sanye da kayan NSCDC domin kauce wa gano su
- Gwamnatin Tarayya ta jaddada janye ‘yan sanda daga rakiya ta manyan mutane domin ƙarfafa tsaro da ayyukan ‘yan sanda a fadin ƙasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta kama jami’an ‘yan sanda huɗu bisa zargin bayar da rakiya ga wani babban mutum a kasa.
Sojojin sun ɗauki wannan mataki ne da suke ganin ya saba wa umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar.

Source: Facebook
TABLE OF CONTENTS
Majiyoyin ‘yan sanda sun shaida wa Zagazola Makama cewa an kama jami’an ne ranar 17 ga Disambar 2025 da misalin karfe 9:30 na safe.
Umarnin da Tinubu ya ba yan sanda
Tun farko Shugaba Tinubu ya umarci janye yan sanda daga gadin manyan mutane a Najeriya duba da matsalolin da ake ciki na tsaro.
Tinubu ya bukaci masu sha'awar neman jami'an tsaro da za su yi gadinsu su nemi jami'an hukumar NSCDC.
Lamarin ya jawo magana daga yan adawa da suke ganin duk siyasa ce saboda an sha ba da umarnin amma ba ta aiki.
Yadda aka kama yan sanda a Abuja
Rahoton ya nuna cewa jami’an suna kan aikin rakiya ne lokacin da sojoji suka cafke su bisa karya dokar shugaban kasa.
An bayyana sunayen jami’an da aka kama da suka hada da ASP Musa Waziri da Insfekta, Jeremiah Achimogu na 45 PMF Abuja.
Sauran jami’an da aka kama sun hada da Insfekta Awipi Terry na 21 PMF da kuma InsfektaHassan Baba na 50 PMF Abuja.
Majiyoyin tsaro sun ce jami’an sojoji ne suka kama ‘yan sandan bayan sun karya umarnin janye jami’an tsaro daga rakiyar manya.

Source: Facebook
Salon yaudarar da jami'an suka yi
Rahotanni sun ce jami’an sun sanya kayan da suka yi kama da na NSCDC domin yaudarar jami’an tsaro da kauce wa gano su.
Tun bayan cafke su, an tsare jami’an, sannan aka fara daukar matakan ladabtarwa a kansu bisa ka’idojin aiki da doka.
Gwamnatin Tarayya ta riga ta bayar da umarnin janye ‘yan sanda daga rakiyar manya domin mayar da su kan tsaron cikin gida, cewar Channels TV.
An ce matakin na da nufin ƙarfafa ayyukan ‘yan sanda da kuma inganta tsaro a fadin Najeriya baki daya.
An gargadi yan sanda kan gadin manya
Mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa duk jami’in da aka kama yana tsaron manyan mutane zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Babban sufetan 'yan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci kwamishinoni su kama duk jami'in da ya karya wannan sabuwar doka.
Tun da fari, Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin janye 'yan sanda daga manyan mutane, inda aka ce su koma amfani da jami'an NSCDC.
Asali: Legit.ng

