An Fara Surutu kan Kungiyoyin da Gwamnatin Tinubu Ta Ce Sun Zama 'Yan Ta'adda
- Masana harkokin tsaro sun fara raddi kan matakin gwamnatin tarayya na ayyana wasu kungiyoyi a matsayin 'yan ta'adda
- Shugaban kamfanin Beacon Consulting Ltd, Kabiru Adamu ya yi fatali da jawabin Ministan Yada Labarai da Wayar da kan Jama'a
- Ya ce kotuna kadai ke da hurumin ayyana kungiyoyi a matsayin 'yan ta'adda, ba shugaban kasa ko wani minista ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani masani kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya yi fatali da matakin gwamnatin tarayya na ayyana wasu kungiyoyi a matsayin na 'yan ta'adda.
Kabiru Adamu ya bayyana cewa ikon ayyana wata ƙungiya a matsayin ta ta’addanci yana hannun kotuna ne kaɗai, ba shugaban kasa ko wani minista ba.

Source: Twitter
Kabiru Adamu ya fadi haka ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV a ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, 2025.

Kara karanta wannan
A karshe, Gwamnatin Tarayya ta bayyana kungiyoyi da take kallo a matsayin 'yan Ta'adda a Najeriya
Matakin gwamnati da ya jawo surutu
Masanin ya yi wannan bayani ne a matsayin martani ga jawabin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris.
A jiya Litinin, Ministan ya sake nanata furucin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa daga yanzu ’yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, za a riƙa ɗaukar su a matsayin ’yan ta’adda.
Mohammed Idris ya ce manufar wannan tsari ita ce ƙarfafa musayar bayanan sirri da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.
Ya ce duk wata kungiya da ta dauki makami, take sace yara, farmakar manoma da hana mutane zaman lafiya ta zama kungiyar ta'addanci.
Masanin tsaro ya yi fashin baki kan matakin
Da yake martani kan wannan mataki, Kabiru Adamu, wanda shi ne shugaban kamfanin Beacon Consulting Ltd, ya ce dokokin Najeriya ba su bai wa bangaren zartarwa ikon ayyana ƙungiya a matsayin ta ta’addanci ba.
Ya ce:
“Dokar da ke fayyace wanene ɗan ta’adda a Najeriya ita ce Dokar Hanawa da Yaƙi da Ta’addanci, wadda aka yi mata kwaskwarima a shekarar 2022.
“Dokar ta bayyana abin da ake kira ta’addanci, sannan ta tanadi hanyoyin da ake bi wajen tantance ko wata ƙungiya ta cancanci a ayyana ta a matsayin ƙungiyar ta’addanci, ko kuma wanda ke tallafawa ko ɗaukar nauyin ta’addanci.
“Wannan doka ta ɗora nauyin yanke wannan hukunci a kan kotun da ke da hurumi, kuma ta bai wa Antoni Janar na Tarayya alhakin gabatar da ƙara ko buƙata a gaban kotu."
"Tinubu ba shi da iko" - Kabiru Adamu
Bisa haka, Kabiru Adamu ya jaddada cewa shugaban kasa ba shi da hurumin ayyana wata kungiya ko gungun mutane a matsayin 'yan ta'adda, cewar Vanguard.
"Saboda haka, ko Shugaban ƙasa ma ba shi da ikon ayyana wata ƙungiya a matsayin ta’addanci, haka nan babu wani mamba na bangaren zartarwa da ke da wannan iko. Ikon yana hannun bangaren shari’a ne, ta hannun kotu,” in ji Adamu.
Masani kan tsaron ya kuma nuna damuwa cewa idan aka bai wa bangaren zartarwa ikon ayyana ƙungiyoyi a matsayin ’yan ta’adda, hakan na iya zama siyasa, wanda zai zama barazana ga dimokuraɗiyya.

Source: Twitter
Tinubu ya kafa sabon tsarin tsaro
A baya, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta fara aikin kafa sabon tsarin tsaron kasa domin murkushe ta'addanci gaba daya.
Ya ce daga yanzu duk wata ƙungiya ko mutune da ke ɗauke da makamai ba tare da lasisi ba, za a riƙa ɗaukar su a matsayin ’yan ta’adda.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya kan masu aikata laifuffuka kaɗai ba, za ta fuskanci masu ɗaukar nauyinsu da masu ba su tallafi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

