Dalilin da Ya Sa Simintin Dangote Ya Fi Araha a Kasashen Waje Fiye da Najeriya
- Attajirin Afirka, Aliko Dangote ya yi bayani kan dalilin da ya sa farashin simintin kamfaninsa ya fi sauƙi a ƙasashen waje, fiye da abin da ake saye a gida
- Ya danganta bambancin farashin da yawan haraji da tsauraran ƙa’idoji da masana’antu ke fuskanta a Najeriya, wanda ke ƙara tsadar kayayyaki
- Dangote ya ce irin wannan matsala ne ke kewaye da matatarsa da ke Legas, wadda duk da manufarta ta rage matsalar mai take fuskantar suka daga wasu ɓangarori
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Aliko Dangote, wanda aka fi sani da attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, ya shahara wajen jaddada muhimmancin masana’antun cikin gida a matsayin hanyar samun ’yancin kai a tattalin arzikin Najeriya.
Kamfanoninsa a fannoni daban-daban kamar siminti, sukari da man fetur sun kasance ginshiƙan habaka masana’antu na ƙasar nan.

Source: Getty Images
Business Insider Africa ta ce ya amsa tambaya kan dalilin da ya sa kayayyakin Dangote, musamman siminti, ke yawan zama masu rahusa a ƙasashen waje fiye da a kasuwar Najeriya.
Tambaya ta biyu kuma ita ce dalilin da ya sa matatar Dangote, wadda aka gina domin rage matsalar makamashi, ke fuskantar turjiya daga wasu ’yan ƙasar.
Dangote ya yi ƙoƙarin amsa waɗannan tambayoyi a wani taron manema labarai, inda ya bayyana ra’ayinsa kan yadda tsarin haraji da ƙa’idoji ke shafar farashin kayayyakin da ake samarwa a Najeriya.
Dalilin arahar simintin Dangote a waje
Dangote ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa simintin da yake fitarwa waje ya fi rahusa shi ne tsadar haraji da kamfanoni ke biya a cikin gida.
Ya ce idan ana fitar da kaya zuwa ƙasashen waje, kamfaninsa na tsallake biyan wasu manyan haraji da kudi da ke ƙara tsadar samar da kaya a Najeriya.
A cewarsa, a lokacin fitar da kaya, ba ya biyan harajin shiga na kashi 30 cikin 100, ba ya biyan wasu kaso da ake warewa ilimi da lafiya, haka kuma ba ya biyan harajin VAT da sauransu.
'Dan kasuwar ya ce waɗannan kuɗi suna taruwa ne su ƙara nauyi a kan farashin simintin da ake sayarwa a gida Najeriya
Dangote ya jaddada cewa idan aka rage waɗannan haraji, zai iya sayar da simintin Najeriya cikin sauƙi a kasuwannin duniya, yana gogayya da ƙasashe kamar Turkiyya, Rasha da China.
Yadda haraji ke shafar talakan Najeriya
Dangote ya ce idan aka duba lamarin, ’yan ƙasa ne ke ɗaukar nauyin haraji da gazawar tsarin gudanarwa, lamarin da ke hana kayayyakin cikin gida zama masu araha kamar yadda ake fata.

Source: UGC
Vanguard ta rahoto Dangote ya ce jerin layukan mai sun addabi Najeriya tun shekarun 1970, kuma matatar tasa ta zo ne domin kawo ƙarshen wannan matsala amma tana fama da irin matsalar a yanzu.
'Yan kasuwar mai sun bi sahun Dangote
A wani labarin, kun ji cewa 'yan kasuwar da dillalan man fetur sun bi sahun Alhaji Aliko Dangote wajen rage farashin mai.
A makon da ya wuce matatar Dangote ta rage kudin man fetur tare da cewa za ta cigaba da kawo wa 'yan Najeriya sauki.
Lamarin ya sanya jama'a kauracewa gidajen mai masu tsada, hakan ya sa 'yan kasuwa rage farashi domin jawo kwastomomi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


