A Karshe, Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Kungiyoyi da Take Kallo a Matsayin 'Yan Ta'adda a Najeriya
- A hukumance, gwamnatin tarayya ta bayyana kungiyoyin da ta fara kallo a matsayin na 'yan ta'adda a karkashin sabon tsarin yaki da ta'addanci
- Ministan Harkokin Yada Labarai, Mohammed Idris ya ce maganar rudani kan sunayen kungiyoyin 'yan ta'adda ya kare a Najeriya
- Ya kuma tabbatar da cewa an ceto sauran daliban da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a harin da suka kai makarantar Katolika a jihar Neja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin tarayya ta bayyana kungiyoyin da ta fara dauka matsayin 'yan ta'adda a hukumance a Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana cewa daga yanzu, duk wata kungiya da ta dauki makami, take sace yara, farmakar manoma da sauran nau'ikan razana al'umma, za a dauke su a 'yan ta'adda.

Source: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron manema labarai yau Litinin.

Kara karanta wannan
Buhari, Dahiru Bauchi da mutanen da Tinubu ya mayar da sunayen jami'o'i zuwa sunan su
Minista ya jero kungiyoyin 'yan ta'adda
Ya jaddada cewa lokacin amfani da sunaye masu haddasa rudani ya wuce, duk wata kungiya mai garkuwa da mutane ko kai hare-hare, za a dauke ta kungiyar ta'addanci.
“A bangaren tsaro, a 2025 aka ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin kasa, kuma a watanni masu zuwa za a fara daukar jami’an sojoji da ‘yan sanda. Sannan za a tura jami'an gadin daji su kare mana dazuzzuka.
"Har ila yau, a 2025, mun kafa sabon tsarin yaki da ta’addanci, wadda ya ta’allaka kan ginshikai hudu masu muhimmanci, daukar umarni a wuri guda, bayanan sirri, kwanciyar hankalin al’umma, da yaki da 'yan tawaye."
“Bari in fayyace abin da hakan ke nufi: daga yanzu, duk wata kungiya mai dauke da makamai da ke sace ‘ya’yanmu, kai wa manomanmu hari, ko razana al’ummominmu, za a dauke ta a hukumance a matsayin kungiyar ta’addanci.
- Mohammed Idris.
Matakan da gwamnatin Tinubu ke dauka
Ministan ya kuma bayyana kudurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na shawo kan matsalar tsaro, kamar yadda aka gani a cikin kasafin kudin 2026 da kuma ayyana dokar ta-baci kan tsaro.
Mohammed Idris, wanda aka gani cikin fara'a da annashuwa, ya kuma tabbatar da ceto sauran dalibai 130 da aka sace daga Makarantar Katolika ta St. Mary’s a garin Papiri, Jihar Neja.
Ya ce an samu nasarar ceto duka daliban ne sakamakon kokarin da hukumomin tsaron kasar nan suka yi, kamar yadda Tashar Channels tv ta ruwaito.

Source: Twitter
Tinubu ya shirya tunkarar batun tsaro
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin ci gaba da yaki da ta'addanci domin tabbatar da samun zaman lafiya a fadin kasar nan.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta nuna tausayi ko sassauci ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ba.
Ya ce gwamnati ta sake fasalin tsarin tsaron ƙasa gaba ɗaya domin magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
Asali: Legit.ng
