Minista: 'Yadda Najeriya Ta Magance Sabanin Diflomasiyya tsakaninta da Amurka'

Minista: 'Yadda Najeriya Ta Magance Sabanin Diflomasiyya tsakaninta da Amurka'

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa rikicin diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka ya lafa bayan tattaunawa mai zurfi
  • Rikicin ya samo asali ne daga kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan zargin ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya
  • Domin tabbatar da sulhu, Najeriya da Amurka sun kulla yarjejeniyar kiwon lafiya ta shekaru biyar da ta kai dala biliyan 5.1

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa rikicin diflomasiyya da ya taso tsakaninta da Amurka ya lafa matuka bayan doguwar tattaunawa da fahimtar juna tsakanin kasashen biyu.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai na karshen shekara da aka gudanar a Abuja.

Minista ya fadi yadda Najeriya ta kwantar da tarzomar diflomasiyya tsakaninta da Amurka.
Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris, ya na jawabi ga mahalarta wani taro. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

Rikicin diflomasiyyar Najeriya da Amurka

Kara karanta wannan

An ware Musulmi a gefe da Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar $2bn da Amurka

Ministan ya ce rikicin ya biyo bayan kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, inda ya zargi Najeriya da yi wa Kiristoci kisan gilla tare da yin barazanar daukar matakin soji, in ji rahoton Punch.

A cewar Mohammed Idris, gwamnatin Najeriya ta tunkari lamarin cikin hikima da mutunci, ta hanyar tattaunawa mai gamsarwa da bangaren Amurka.

“Rikicin diflomasiyya da Amurka da ya taso kwanan nan ya lafa sosai sakamakon tattaunawa mai karfi da mutunta juna, wanda ya kai ga karfafa alakar kasashen biyu,” in ji ministan.

Yarjejeniya tsakanin Najeriya da Amurka

A matsayin alamar kyautatuwar alaka, Mohammed Idris ya bayyana cewa Najeriya da Amurka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kiwon lafiya ta shekaru biyar da darajarta ta kai dala biliyan 5.1.

A karkashin yarjejeniyar:

  • Amurka za ta bayar da dala biliyan 2.1 a matsayin tallafi kyauta
  • Najeriya kuma za ta zuba dala biliyan 3

Ministan ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mafi girman hadin gwiwar zuba jari da wata kasa ta taba yi karkashin shirin kiwon lafiyar Amurka na duniya (AFGHS).

Mohammed Idris ya ce yarjejeniyar za ta; inganta ayyukan kiwon lafiya, ceci rayukan ‘yan Najeriya, jawo karin zuba jari daga kasashen waje

Kara karanta wannan

Kasar Amurka ta janye maganar turo dakarun sojoji Najeriya

Ya kara da cewa wannan ci gaba ya nuna cewa fargabar rugujewar alakar Najeriya da Amurka ba ta da tushe, in ji rahoton Premium Times.

Najeriya ta kawo karshen rikicin diflomasiyyarta da Amurka cikin hikima
Shugaban Amurka, Donald Trump da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: @officialABAT, @realDonaldTrump
Source: Getty Images

Najeriya na kara karfi a fagen diflomasiyya

Ministan ya jaddada cewa Najeriya na kara nuna kanta a matsayin kasa mai karfin gwiwa da dabarun diflomasiyya a duniya, wadda ke kare muradunta tare da gina alaka mai amfani da sauran kasashe.

Dangane da batun wakilcin diflomasiyya, Idris ya ce sababbin jakadun Najeriya da aka nada za su kama aiki a kasashen da aka tura su a shekarar 2026, bayan kammala tantancewa da amincewar majalisar tarayya.

Mohammed Idris ya ce hakan zai kara karfafa alakar diflomasiyya da kuma inganta mu’amalar Najeriya da sauran kasashen duniya.

'Dan majalisar Amurka ya shiga coci a Abuja

A wani labari, mun ruwaito cewa, dan majalisar Amurka, Bill Huizenga, ya ziyarci wata coci a birnin tarayya Abuja, a yayin da suke tattaunawa da gwamnatin Najeriya.

Bill Huizenga ya shaidawa al'ummar Kirista cewa 'yan majalisar Amurka za su yi duk mai yiwuwa don kawo karshen kashe su da ake yi da hana su yin ibada cikin nutsuwa.

'Dan majalisar ya ce suna kan tattaunawa da gwamnatin Najeriya domin ganin an magance matsalar tsaro da ke barazana ga addinin Kiristanci da wasu tsirarin Musulmi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com