'Yan Bindiga Sun Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matafiya Masu Zuwa Mauludi a Plateau
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi wa motar wasu matafiya kwanton bauna a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau
- Tsagerun 'yan bindgan sun yi awon gaba da dukkanin matafiyan da ke cikin motar wadanda ke kan hanyar zuwa wajen Mauludi
- Daga cikin mutanen da aka sace har da jinin sarauta da wani malamin addini wadanda ke jagorantar tafiyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 28 a yayin da suke tsaka da tafiya a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun sace mutanen ne daga kauyen Zak, da ke gundumar Bashar, a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce wani shugaban matasa a Wase, Sapi’i Sambo, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho.
'Yan bindiga sun sace matafiya a Plateau
Sapi'i Sambo ya bayyana cewa mutanen da aka sace sun haɗa da maza, mata da kananan yara.
Wani mazaunin garin Bashar, Ibrahim Musa, ya bayyana cewa har yanzu ba a san inda aka kai wadanda aka sace ba.
A cewar shugaban matasan, an sace matafiyan ne a daren ranar Lahadi, 20 ga watan Disamban 2025 yayin da suke kan hanyarsu daga kauyen Zak zuwa al’ummar Sabon Layi domin halartar bikin Mauludi.
An sace jinin sarauta a harin
Sapi'i Sambo ya kara da cewa ’ya’yan sarauta guda biyu da kuma wani malamin addini da ke jagorantar tafiyar suna cikin waɗanda aka sace.
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare, lokacin da suke kan hanyarsu zuwa Sabon Layi domin taron."
"Yan bindigan sun yi wa motar kwanton bauna a wajen garin, suka kwashe dukkan matafiyan, ciki har da yara, suka bar motar a wurin.”
"Da safiyar ranar Litinin ne matafiya a kan hanyar suka hango motar, wadda take mallakin shugaban al’ummar Zak."
"Bayan fara bincike ne aka gano cewa ita ce motar da ke ɗauke da matafiyan da aka sace, wadda aka tare a hanya.”
- Sapi'i Sambo
Shugaban matasan ya ce duk kokarin gano inda aka kai mutanen bai yi nasara ba, yana mai karawa da cewa an sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Source: Original
Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Plateau, SP Alabo Alfred, ya ce suna bincike kan rahoton faruwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa satar mutane, ayyukan ’yan bindiga da satar shanu sun yi kamari a Wase, inda mazauna yankin ke kira ga hukumomin tsaro da su kakkabe ’yan ta’adda da ke addabar yankin.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun bude wuta kan masu hakar ma'adanai a jihar Plateau.

Kara karanta wannan
Ba a gama murnar cin zabe ba, yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman da kansiloli 2
'Yan bindigan sun aikata danyen aikin ne a wani ramin hakar ma'adanai da ke garin Ratoso Fan, a karamar hukumar Barkin Ladi.
Rahotanni sun nuna cewa akalla masu hakar ma'adai 12 aka tabbatar da sun rasa rayukansu a harin da tsagerun 'yan bindigan suka kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


