Mutane Sun Yi kan Wani Mutumi da Ake Zargi da Wulakanta Alkur'ani a Jihar Kano
- 'Yan sanda sun kubutar da wani mutumi da ake zargi da yaga Alkur'ani Mai Girma a wani masallaci a Unguwar Badawa ta jihar Kano
- Rahoto ya nuna cewa mutumin mai suna, Musa Tasiu ya shiga masallaci a otal, ya fasa gilashi, sannan ga dauki kwafin Alkur'ani ya yaga
- Majiyoyi sun ce nan take mutane suka taru da nufin hallaka mutumin amma dakarun yan sanda suka shiga tsakani a daren jiya Lahadi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Mutane sun fusata, sun yi yunkurin hallaka wani mutumi da ake zargin ya wulakanta Alkur'ani Mai Girma a jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa dakarun ‘yan sandan jihar Kano sun yi nasarar ceto mutumin mai suna, Musa Tasiu daga yunkurin mutane na kashe shi.

Source: Original
Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rahoto da ya wallafa a shafinsa na X.
Hukumar yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar cewa ta ceci mutumin daga gungun mutane, biyo bayan zarginsa da wulakanta Alkur'ani a wani otel da ke unguwar Badawa a birnin Kano.
Abin da mutumin ya yi wa kwafin Alkur'ani
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru a kimanin ƙarfe 9:45 na dare a ranar 21 ga Disamba, 2025 a Sarina Hotel da ke unguwar Badawa Quarters.
A cewar majiyar, an samu kira na gaggawa cewa wasu maza uku, Musa Tasiu, Awwal Ibrahim, da Soja Snu, dukkansu daga Dorayi, sun je shan shisha a otel din Sarina.
Majiyar ta ce ɗaya daga cikin wadanda ake zargi, Musa Tasiu, ya shiga masallacin otal din, ya karya ƙofar gilashi, ya ɗauki kwafi na Al-Qur’ani Mai Girma sannan ya yaga shi.
Matakin da mutane suka yi niyyar dauka
“Bayan faruwar lamarin, mutane suka taru da yawa a cikin wurin, kuma da alama wanda ake zargin suka so su farmaka, su dauki doka a hannunsu," in ji majiyar.
Sai dai Zagazola Makama ya tabbatar da cewa tawagar 'yan sanda da ke sintiri a yankin ce ta samu nasarar ceton mutumin daga shirin wadannan mutane da suka fusata.

Source: Getty Images
Majiyoyin sun ce wata tawagar sintiri da ke karkashin sashen amsa kiran gaggawa a rundunar 'yan sandan Kano, ce ceci wanda ake zargi, sannan ta dawo da zaman lafiya da lumana a yankin.
Majiyar ta kara da cewa yanzu al'amura sun koma daidai bayan faruwar lamarin, yayin da yan sanda ke ci gaba da bincike kan abin da ya faru.
Matasa sun kashe dan sanda a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne sun kashe jami'in dan sanda da ke bakin aiki a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Rahotanni sun nuna cewa matasan sun farmaki dan sandan ne a kusa da yankin Arakale bayan wata takaddama da ta tashi tsakaninsu.
Kakakin rundunar yan sanda ya bayyana cewa jami’in yana cikin aikin sintiri ne da sassafe lokacin da ya hadu da wasu bara-gari da ke son tayar da rigima.
Asali: Legit.ng

