Buhari, Dahiru Bauchi da Mutanen da Tinubu Ya Mayar da Sunayen Jami'o'i zuwa Sunan Su

Buhari, Dahiru Bauchi da Mutanen da Tinubu Ya Mayar da Sunayen Jami'o'i zuwa Sunan Su

Sauya sunan jami'ar tarayya ta Azare da shugaba Bola Tinubu ya yi zuwa sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya jawo nazari kan jami'o'in da aka sauya wa suna a karkashin mulkinsa.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tun bayan hawansa mulki a 2023, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan wasu jami'o'in tarayya a Najeriya.

A karshen makon da ya wuce ne aka sauya sunan jami'ar gwamnatin tarayya da ke Azare a jihar Bauchi zuwa sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Bola Tinubu, Muhammadu Buhari, Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Shugaba Bola Tinubu, Sheikh Dahiru Bauchi da Muhammadu Buhari. Hoto: Nazir Tahir|Bayo Onanuga|Bashir Ahmad
Source: Facebook

A wannan rahoton, Legit Hausa ta hada rahoto na musamman game da jami'o'in da shugaba Bola Tinubu ya sauya wa suna a Najeriya.

1. Tinubu ya sauya sunan jami'ar Abuja

NUC ta wallafa cewa a Disambar 2024 shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa Jami’ar Yakubu Gowon.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rada wa babbar jami'a a Najeriya sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Ya dauki wannan mataki ne domin girmama tsohon shugaban kasa na mulkin soja a Najeriya, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), a lokacin ya cika shekaru 90 a duniya.

Janar Yakubu Gowon mai ritaya
Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ga 'yan jarida a fadar shugaban kasa, bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a 2024.

A cewar Ministan, sauya sunan jami’ar na nufin amincewa da gudunmawar da Yakubu Gowon ya bayar wajen tabbatar da hadin kan Najeriya da kuma jajircewarsa wajen ci gaban kasa.

2. Tinubu ya sa wa jami'a sunan Maitama

A watan Marisa na 2025, shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Kano zuwa Yusuf Maitama Sule.

Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen cigaban zamantakewa da siyasar Najeriya a tsawon rayuwarsa mai cike da ayyuka na alheri.

Fadar shugaban kasa ta wallafa cewa ya taba zama wakilin dindindin na Najeriya a majalisar dinkin duniya da ke New York, inda ya rike mukamin shugaban kwamiti na musamman.

Yusuf Maitama Sule
Marigayi, Alhaji Yusuf Maitama Sule. Hoto: Hassan Mohammed
Source: UGC

Haka kuma, ya taba zama jagoran tawagar Najeriya a taron kasashen da suka samu ‘yancin kai a shekarar 1960, kwamishinan tarayya na farko mai kula da karbar korafe-korafe na Jama’a a shekarar 1976.

Kara karanta wannan

Tsofaffin 'yan majalisa sun kawo wanda suke fatan ya zama gwamnan Kano a 2027

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ɗaukaka tarihin Ambasada Yusuf Maitama Sule ta hanyar sanya sunansa a jami’ar zai zama abin koyi ga matasa, tare da karfafa su kan rikon amana, kishin kasa, kyawawan dabi’u da kuma kishin al’umma.

3. An mayar da Unimaid jami'ar Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari domin girmama marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Marigayi Buhari ya rasu yana da shekaru 82 a duniya a wani asibiti da ke birnin London, bayan fama da matsalolin lafiya.

Kofar shiga jami'ar Maiduguri
Wani sashe na kofar shiga jami'ar Maiduguri da ke Borno. Hoto: University of Maiduguri
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya sanar da sauya sunan jami’ar ne a yayin wani zama na musamman na majalisar zartarwa a watan Yulin 2025.

Premium Times ta rahoto ya ce:

“Don girmama tarihinsa da tunawa da shi, shin wannan zama na musamman na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) zai amince da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa Jami’ar Muhammadu Buhari, Maiduguri?”

Sai dai ana sa ran majalisar dokoki za ta yi gyara ga dokar da ta kafa jami’ar. A halin da ake ciki kuma, kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU reshen jami’ar ta yi watsi da wannan kudiri.

Kara karanta wannan

Ba a gama murnar cin zabe ba, yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman da kansiloli 2

4. An sa wa jami'a sunan Dahiru Bauchi

A Disamban 2025, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Jami’ar kimiyyar lafiya ta tarayya da ke Azare, jihar Bauchi, zuwa sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin karrama marigayin.

An bayyana wannan sanarwa ne a yayin ziyarar ta’aziyyar da shugaba Tinubu ya kai wa gwamnatin jihar Bauchi da kuma iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Shugaba Bola Tinubu a gidan Dahiru Bauchi
Gwamnan Bauchi da Bola Tinubu a gidan Dahiru Bauchi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya bayyana irin gagarumar gudunmawar da marigayi malamin ya bayar, yana mai cewa girmamawar da aka yi masa ta dace da irin tarihinsa.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya bayyana godiyarsa sosai ga shugaban kasa bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai da kansa.

An sace daliban jami'a a jihar Rivers

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wa jami'ar RSU da ke jihar Rivers.

Rahotanni sun nuna cewa an kama wasu daga cikin dalibai kuma an tafi da wasu cikin daji yayin farmakin da aka kai.

Wani dalibi da ya tsallake rijiya ta baya ya shaida wa manema labarai cewa maharan sun shiga gidan da suke kwana ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng