Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekarar 2026
- Lokacin bukukuwan Kirsimeti ta shekarar 2025 da sabuwar shekara mai kamawa na ci gaba da kara karatowa
- Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutu guda biyu domin bukukuwan wadanda suke zuwa a karshen shekara
- Hakazalika ta ayyana ranar Alhamis, 1ga watan Janairun 2025 a matsayin ranar hutu don murnar shigowar sabuwar shekara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ayyana ranakun hutu don bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Alhamis, 25 ga Disamba, da Jumma’a, 26 ga Disamba, 2025 a matsayin ranakun hutu domin bikin Kirsimeti da ranar ba da kyaututtuka.

Source: Twitter
Wannan sanarwa na kunshe ne a cikin wata takarda da babbar sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr. Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin, 22 ga watan Disamban 2025, wadda tashar NTA ta sanya a shafin X.

Kara karanta wannan
Kungiyar CAN ta yi magana da babbar murya ga Tinubu yayin da ake shirin Kirsimeti
Gwamnatin tarayya ta ba da hutu?
Babbar sakatariyar ta fitar da sanarwar ne a madadin Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo.
Haka kuma, gwamnatin ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Janairu, 2026 a matsayin ranar hutun sabuwar shekara.
A cewar sanarwar, Ministan ya bukaci ’yan Najeriya da su yi tunani kan muhimmancin kauna, zaman lafiya, tawali’u da sadaukarwa da ke tattare da haihuwar Yesu Almasihu, jaridar The Punch ta dauko labarin.
Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga ’yan kasa da su yi amfani da wannan lokacin bukukuwa wajen addu’ar neman zaman lafiya, ingantaccen tsaro da ci gaban kasa, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
Ya kara da ba da shawara ga ’yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda, tare da kula da batun tsaro a lokacin bukukuwan, yana mai yi musu fatan barka da Kirsimeti da kuma sabuwar shekara mai albarka.
Wadanne ranaku aka ware don hutu?
"Gwamnatin tarayya ta ayyana Alhamis, 25 ga Disamba, 2025; Jumma’a, 26 ga Disamba, 2025; da Alhamis, 1 ga Janairu, 2026 a matsayin ranakun hutun gwamnati domin bikin Kirsimeti, Boxing Day da Sabuwar Shekara bi da bi."
“Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayar da wannan sanarwa a madadin gwamnatin tarayya, ya mika sakon barka da gaisuwar Kirsimeti da Sabuwar Shekara ga Kiristoci a Najeriya da ma duniya baki ɗaya."
"Tare da gaishe da dukkan ’yan Najeriya yayin da suke murnar ganin karshen shekara da farkon sabuwa."
“Lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara na ba ’yan Najeriya dama wajen karfafa ɗorewar zumunci, nuna tausayawa ga juna, da kuma sabunta kudurin haɗin gwiwa wajen gina kasa."
“Ministan na yi wa dukkan ’yan Najeriya barka da Kirsimeti da kuma sabuwar shekara mai albarka.”
- Dr. Magdalene Ajani

Source: Facebook
Gwamnatin tarayya ta ba da hutu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ayyana lokacin hutu don zagayowar ranar ma'aikata ta duniya.
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Mayun 2025 domin bikin ranar ma’aikata wadda ake gudanarwa a kowace shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo wanda ya fitar da sanarwar ya jaddada buƙatar zaman lafiya domin haɓaka masana’antu da ci gaban tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
