Rigima Ta Ki Karewa: Shugaban Majalisa, Akpabio Ya Maka Natasha a Kotun Koli
- Godswill Akpabio ya garzaya kotun koli domin kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kan shari’ar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a majalisa
- Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar ne bisa kura-kuran tsari da suka shafi dokokin gabatar da takardu, abin da ya tayar da muhawara a fagen shari’a
- Matakin Akpabio na shiga shari’ar da kansa ya kara jan hankalin jama’a, musamman ganin yadda rikicin siyasa tsakaninsa da Sanatar ya dade yana ci gaba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya nemi shiga kotun koli domin kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke dangane da dakatar da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.
Takardun kotu da aka sanya wa kwanan wata 1, Disamba, 2025, sun tabbatar da cewa Akpabio ya shigar da kara ne bayan kotun daukaka kara ta yi watsi da takardar karar da gwamnatin tarayya ta gabatar a baya.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa hukuncin kotun ya zo ne a cikin rikicin shari’a da siyasa da ya dabaibaye dakatar da Natasha, lamarin da ke kara tayar da kura a majalisar dattawa da ma tsakanin jama’a.
Natasha Akpoti ta yi nasara kan Godswill Akpabio
Kotun daukaka kara ta bayyana cewa takardar karar da aka gabatar ba ta cika ka’idojin doka ba, musamman ka’idojin da ke cikin dokokin kotun game da tsari da rubutu.
Alkalan sun ce an karya dokoki da dama, ciki har da amfani da yanayin girman rubutu da tazarar layi da ba su dace ba.
Haka kuma, kotun ta lura cewa shafukan takardar sun haura iyakar da doka ta tanada, ba tare da an nemi izinin kotu ba. Baya ga haka, sanarwar daukaka karar kanta an same ta da kura-kurai da suka shafi ingancinta.
Kotun ta yanke cewa wadannan kura-kuran ba kanana ba ne, manyan matsaloli ne da suka shafi sahihancin karar gaba daya, wanda hakan ya sa aka yi watsi da ita baki daya.
Akpabio ya kai Sanata Natasha kotun koli
Bayan rashin gamsuwa da hukuncin, Akpabio ya nemi kotun koli da ta soke hukuncin da aka yanke a ranar 28, Nuwamba, 2025.
The Cable ta rahoto cewa a cikin sanarwar daukaka karar da ya gabatar, ya ce an tauye masa hakkin sauraron korafe-korafensa.
Ya yi ikirarin cewa kotun daukaka kara ta ki ba shi damar gyara kura-kuran takardar ko kuma neman izinin wuce iyakar shafuka, abin da ya ce ya sabawa adalci.

Source: Facebook
Masu lura da al’amura sun ce shiga shari’ar da kansa da shugaban majalisar dattawa ya yi abu ne da ba kasafai ake gani ba, lamarin da ya kara jawo muhawara a tsakanin lauyoyi da ‘yan siyasa.
Majalisa ta yi gyara kan dokokin zabe
A wani labarin, kun ji cewa majalisar wakilai ta fara gyara game da dokokin zabe kafin zaben shekarar 2027 mai zuwa.
A wani mataki na kara sahihancin zabe, majalisar ta kara kudin da 'yan siyasa za su iya kashewa yayin yakin neman zabe.
Masana harkokin zabe sun nuna damuwa kan cewa karin kudin zai iya hana talakawa masu nagarta damar shiga siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

