MRS: An Sauke Farashin Man Fetur a Jihohin Najeriya, Lita Ta Koma Ƙasa da N740

MRS: An Sauke Farashin Man Fetur a Jihohin Najeriya, Lita Ta Koma Ƙasa da N740

  • Matatar Dangote ta fara sayar da man fetur a kan farashin ₦739 kan kowace lita a dukkan gidajen mai na MRS a faɗin Najeriya
  • An sauke farashin ne domin rage wahala ga ’yan Najeriya musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
  • Matatar Dangote ta gargadi masu ƙoƙarin ƙirƙirar ƙarancin man fetur tare da kira ga hukumomi su ɗauki tsauraran matakai a kai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Matatar Dangote ta sanar da fara sayar da litar man fetur, a kan farashin ₦739 a dukkan gidajen mai na kamfanin MRS Oil Nigeria Plc da ke faɗin ƙasar.

A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi, sabon farashin zai fara aiki a dukkan gidajen man MRS sama da 2,000 a ƙasar, domin tabbatar da cewa rangwamen ya kai ga ’yan Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi nasarar ceto sauran daliban makarantar Neja 130 da aka sace

Matatar Dangote ta fara sayar da fetur kan N739 a gidan man MRS
Alhaji Aliko Dangote da hoton gidan man kamfanin MRS. Hoto: Dangote Industries|MRS Oil and Gas
Source: UGC

Dangote zai sayar da fetur kan N739

Dangote ya bayyana cewa wannan mataki wani gagarumin ci gaba ne wajen samar da man fetur mai araha da kuma daidaita kasuwar man fetur a ƙasar, in ji rahoton Punch.

Matatar ta ce rage farashin litar fetur zuwa N739 a wannan lokaci na bukukuwa ya bambanta da abin da aka saba gani a Najeriya, inda a baya ake fuskantar ƙarancin mai da tsadar farashi musamman a lokutan bukukuwa.

Dangote ya yaba wa kamfanin MRS da sauran masu sayar da mai da suka rungumi sabon tsarin farashi, tana mai kiran sauran kamfanoni da su yi koyi da wannan mataki domin tallafa wa farfaɗowar tattalin arzikin ƙasa.

Tace fetur: Rage dogaro da kasashen waje

A cewar sanarwar da matatar ta fitar:

“Mun yaba wa MRS da sauran ’yan kasuwa da suka nuna kishin ƙasa ta hanyar rage farashin mai. Muna kira ga sauran su bi wannan hanya domin taimaka wa tattalin arzikin Najeriya."

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya gargaɗi gwamnoni game da tsaro a bukukuwan kashen shekara

Matatar ta bayyana cewa ta hanyar tace man fetur a cikin gida, Najeriya na rage dogaro da kasuwannin waje, tare da adana kuɗaɗen waje, kare darajar naira, da ƙarfafa tsaron makamashi.

Kamfanin ya ƙara da cewa yana samar da man fetur har lita miliyan 50 a kowace rana, wanda hakan ke taimakawa wajen kawar da ƙarancin mai da kuma tabbatar da wadatar sa a lokacin bukukuwa.

Matatar Dangote ta roki sauran 'yan kasuwa su rage farashin litar fetur
Matatar Dangote da ke birnin Legas, wacce ke tace lita miliyan 50 na danyen mai a kullum. Hoto: Bloomberg
Source: UGC

Gargaɗi kan ƙirƙirar ƙarancin fetur

Matatar Dangote ta yi gargaɗi mai tsauri ga wasu ’yan kasuwa da ka iya ƙoƙarin ƙirƙirar ƙarancin man fetur domin hana saukar farashi aiki, in ji rahoton Vanguard.

“Duk wani ƙoƙari na ƙirƙirar ƙarancin mai ko wasa da wadatar sa domin hana rage farashi aiki ba kishin ƙasa ba ne. Muna kira ga hukumomi su sanya ido sosai kuma su ɗauki mataki,” in ji matatar.

Kamfanin ya shawarci ’yan Najeriya da su guji sayen man fetur a farashi mai tsada, inda aka tanadi man fetur mai inganci da araha a gidajen MRS.

Rikici ya kaure tsakanin 'yan kasuwar fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rage farashin mai a matatar Alhaji Aliko Dangote ya fara jawo wa 'yan kasuwa da suke sayar da mai da tsada matsala.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi alkawarin da ya yi wa Amurka da Turai kan tsaron Najeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu shigo da mai, mazu rumbunan ajiyar mai da yan kasuwar fetur da gas sun fara kokawa game da saukar farashin kayan.

Ana hasashen matatar Dangote za ta rasa kusan Naira biliyan 91 a wata guda saboda ragin da aka samu, duk da cewa lamarin ya yi wa talakawa dadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com