Rundunar Sojojin Sama Ta Biya Diyya ga Iyalan Bayin Allah da Ta Kashe a Sokoto

Rundunar Sojojin Sama Ta Biya Diyya ga Iyalan Bayin Allah da Ta Kashe a Sokoto

  • Rundunar sojojin saman Najeriya ta biya diyya ga mutanen da hatsarin harin sama ya shafa a ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa a Sokoto
  • Binciken rundunar ya tabbatar da mutuwar fararen hula 13 da raunata wasu takwas sakamakon harin sama da aka kai bisa kuskure
  • Shugaban sojojin ya jaddada cewa kare rayukan fararen hula shi ne ginshiƙin aikinsu, yana mai alƙawarin hana sake faruwar irin wannan hari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Rundunar sojojin saman Najeriya ta sanar da biyan diyya ga mutanen da hatsarin harin sama ya shafa, da kuma iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wani harin sama da aka kai bisa kuskure a ranar 25 ga Disamba, 2024, a jihar Sokoto.

Mutanen da lamarin ya shafa su ne mazauna ƙauyukan Gidan Bisa da Rumtuwa da ke ƙaramar hukumar Silame ta jihar.

Kara karanta wannan

Cakwakiya: Tinubu ya shiga rudani da aka tafka kuskure a taron APC a Aso Rock

Rundunar sojojin sama ta Najeriya ta biya diyyar mutanen da ta kashe a Sokoto.
Wakilan rundunar sojojin sama da Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Kuskuren harin sojoji a garuruwan Sokoto

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Lahadi, aka wallafa a shafin rundunar na X.

Da yake jawabi a madadin shugaban sojojin sama, Air Marshal Sunday Aneke, shugaban hulɗar soja da fararen hula, AVM Edward Gabkwet, ya nuna godiya ga gwamnatin Sokoto bisa kyakkyawar alaƙar da ta gina tsakanin rundunar da al’ummar jihar.

Ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu, kan manufofin ci gaba na bai ɗaya da kuma matakan tsaro da yake aiwatarwa a ƙarƙashin manufar 9-Point Smart, musamman kafa rundunar tsaron al’umma ta jihar Sokoto.

A cewarsa, matakan tsaron da gwamnan ya ɗauka, waɗanda suka ta’allaka da yanayin yankin, sun taimaka matuƙa wajen tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen dakile ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga, tare da inganta tsaro a wasu sassan jihar.

Hafsun sojojin saman ya bayyana cewa harin saman an kai shi ne a ƙarƙashin Operation Fasan Yamma, bayan samun rahotannin leƙen asiri da ke nuna cewa wasu ’yan ta’adda na wucewa ta yankunan da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Amurka ta kai hari ta kashe mutane bayan Trump ya sa wa Najeriya takunkumi

An tabbatar da kuskuren kashe fararen hula

Ya ce duk da an gudanar da binciken leƙen asiri sau da dama kafin kai harin, wani ƙorafi da aka samu a watan Afrilu 2025 ya nuna cewa an kashe fararen hula ne a harin.

“Bayan gudanar da cikakken bincike, an tabbatar da cewa fararen hula 13 sun rasa rayukansu a bisa kuskure, yayin da wasu takwas suka samu raunuka daban-daban,” in ji Air Marshal Sunday Aneke.

Ya ƙara da cewa sakamakon binciken ya matuƙar jefa rundunar a cikin baƙin ciki, lamarin da ya sa aka ɗauki matakin gaggawa domin gyara kura-kuren da suka faru.

Air Marshal Aneke ya jaddada cewa tun bayan zamansa hafsun sojojin sama a ranar 24 ga Oktoba, 2025, ya dauki kare rayukan fararen hula a matsayin muhimmin ginshiƙi a tsarin jagorancinsa.

Ya ce an kafa rundunar sojojin sama ne domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, yana mai cewa babu wata rundunar soja da ke da niyyar cutar da mutanen da aka ɗora mata alhakin karewa.

Kara karanta wannan

Bayan suka ta ko ina, an dakatar da yi wa dogarin Shugaba Tinubu karin girma

Rundunar sojojin sama ta biya diyya ga iyalan fararen hular da ta kashe bisa kuskure
Wasu daga cikin mutanen da suka samu diyya daga rundunar sojoji a Sokoto. Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

An biya diyya da daukar matakan kariya

Ya bayyana cewa biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa na da nufin zama ta’aziyya, tabbatar da ɗaukar alhakin harin, rage tashin hankali, da kuma rufe wannan babi mai raɗaɗi, tare da zama darasi don rage faruwar irin wannan hatsari a nan gaba.

Shugaban sojojin ya kuma bayyana cewa rundunar na ci gaba da ƙarfafa matakan kariya da martani ga illar da fararen hula ke fuskanta, ciki har da ƙirƙirar tsarin NAF-CHMRAP.

A nasa bangaren, gwamnan Sokoto ya nuna godiya ga rundunar bisa jajircewarta wajen kare ’yan ƙasa da kula da jin daɗinsu, tare da yabawa rawar da take takawa wajen samar da tsaro a Najeriya.

Gwamna Ahmed ya ziyarci fararen hula

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ziyarci garuruwa biyu da jiragen yakin sojoji suka yi musu luguden bama-bamai bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun sake yin kuskure, sun hallaka bayin Allah masu yawa a Borno

Akalla mutane 10 ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a wani hari ta sama da ake zargin sojoji sun kai kan fararen hula a karshen Disamba, 2025.

Sakamakon damuwar da ya yi da lamarin, Gwamna Aliyu ya tsallake duk wasu ƙalubale na rashin kyaun hanya, ya ziyarci kauyukan tare da alkawarin yin bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com