Tsohon Minista Ya Gaskata Aisha Buhari game da Mulkin Tsohon Shugaban Ƙasa
- Tsohon Minista, Solomon Dalung ya yi zargin cewa wasu sun ƙwace iko da mulkin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
- 'Dan siyasar ya ce waɗannan mutane shafaffu da mai suna yi fafutuka wajen neman kusanci da tasiri a mulkin marigayi Muhammadu Buhari
- Barista Dalung ya ce zai fayyace dalilan da suka sa marigayin ya lamunci ayyukan ƙarfe-ƙarfa na waɗannan mutane a cikin littafinsa mai zuwa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya yi zargin cewa mulkin marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya faɗa hannun wasu masu iko da ya ce sun baza mulki a matakai daban-daban.
Bayaninsa na zuwa ne bayan rasuwarsa tsohon Shugaban Ƙasan a farkon wannan shekara, tare da muhawarar da ke ƙara ƙarfi kan irin tarihin da ya bari bayan ya ci zamaninsa.

Source: Twitter
Dalung ya bayyana wannan zargi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, inda ya yi waiwaye kan shugabancin Buhari.
Solomon Dalung ya magantu kan mulkin Muhammadu Buhari
A cewar Dalung, akwai wani yunƙuri da aka tsara domin sake wanke Buhari a tarihi, musamman ta hanyar wallafa littattafai da bayanai daga mutanen da suka amfana da gwamnatinsa kawai.
Ya ce wannan yunƙuri na fitowa ne daga tsofaffin mataimaka, muƙarrabai, jami’an gwamnati da kuma ‘yan uwansa domin shafe kura-kuransa a idon ƴan Najeriya
Dalung ya ambaci littafin "From Soldier to a Statesman" na Charles Omole, inda ya ce littafin ya haifar da ce-ce-ku-ce.
Ya ce an yi ta maganganu saboda wasu kalamai da aka danganta da matar Buhari, waɗanda suka shafi lamurra na sirri da na gwamnati.
Dalung ya ce yana magana ne daga kwarewarsa ta kai tsaye ba kame-kame ba, yana mai cewa yana da kusanci da Buhari a lokacin da yake cikin gwamnati.
A cewarsa, wannan kusanci ya jawo masa gaba daga wasu cikin masu zagaye da Shugaban Kasa, musamman ganin yadda suke son kankane komai a gwamnati.
Bangarorin da suka fantama a mulkin Buhari - Dalung
Dalung ya yi zargin cewa iko a cikin gwamnatin Buhari ya kasu kashi uku: ƙungiyar siyasa karkashin jagorancin marigayi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa.
Baya ga bangaren marigayi Abba Kyari, ya ce akwai ƙungiyar iyalinsa da matar Shugaban Ƙasa ke da tasiri a cikinta.
Ta uku kuma daga cikin masu faɗa a ji ita ce gungun cikin gida ta mataimaka da ake daidaita harkokinta ta hannun tsohon mataimakin Buhari, Tunde Sabiu.
Dalung ya ce waɗannan ƙungiyoyi sun zama cibiyoyin iko da ke fafatawa kan samun kusanci, tasiri da iko a wajen shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa duk da rikice-rikicen da ke tsakaninsu, sukan haɗa kai wajen yaƙar duk wanda suka ga barazana ce ga tasirinsu.
Ya ce shi kansa ya zama abin hari daga waɗannan ƙungiyoyi saboda damar da yake da ita ta kai tsaye ga Buhari.

Source: Twitter
Yadda aka rufe wa ministan Buhari kofa
Ya yi zargin cewa a wani lokaci an toshe masa duk wata hanya ta tuntuɓar shugaban ƙasa, ta hukuma da kuma ta bayan fage.
Dalung ya ce bayan wasiku da dama da bai samu amsa ba, Buhari ya shawarce shi da ya rika jira bayan taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa domin su yi magana a sirrance, saboda a cewarsa wasikunsa ba sa isa gare shi.
Ya kuma yi zargin cewa rigimar iko ta fara ne tun da wuri, inda ya ambaci saɓani kan kula da kasafin kuɗin ciyarwa da kula da Fadar Shugaban Ƙasa.
Dalung ya kammala da cewa Buhari ya san an ƙwace masa ikon mulki, amma dalilan da suka sa ya lamunci hakan ko ya kasa dakile shi, zai fayyace su ne a cikin littafin tarihinsa da yake shirin fitarwa.
Aisha Buhari ta faɗi kuskuren mijinta
A baya, kun ji tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta yi bayani kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a tsawon shekaru takwas na mulkin mijinta.
Aisha Buhari ta yi tsokaci mai tsauri kan yadda aka tafiyar da wasu al’amura a lokacin mulkin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023, tana mai cewa akwai kura-kurai.
Ta bayyana cewa rayuwa a cikin fadar Aso Rock ba ta kasance mai sauƙi ba a wasu lokuta, musamman saboda tasirin wasu tsirarun mutane da suka kewaye Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



