'Yan Bindiga Sun Yi Aika Aika bayan Kai Wani Harin Ta'addanci a Zamfara
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a daya daga cikin kauyukan jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma
- Tsagerun 'yan bindigan sun yi jisa tare da yin awon gaba da wasu mutane zuwa cikin daji a harin da suka kai wani kauye na karamar hukumar Bukuyum
- Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta bayyana cewa tana kokarin ceto mutanen da aka sace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - ’Yan bindiga sun kai hari kauyen Fananawa da ke karamar hukumar Bukuyum a jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Asabar, 20 ga watan Disamban 2025 a kauyen na Fananawa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa 'yan bindigan sun kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Al’ummomin Bukuyum sun sha fama da hare-haren kungiyoyin ’yan bindiga a cikin watan da ya gabata, ciki har da wani fashewar bam da ya faru kwanan nan.
Yadda 'yan bindiga suka kai harin
Wani mazaunin yankin, Malam Sani, ya ce miyagun ’yan bindigan sun mamaye kauyen da daddare, suka yi ta ta’asa har zuwa wayewar gari.
"Yan bindiga sun shiga kauyen, suka kashe mutum ɗaya, suka sace mutum bakwai, sannan suka harbi wani mutum guda da ya samu munanan raunuka."
"An tura shi asibitin koyarwa na Sokoto domin samun kulawar gaggawa.”
- Wani mazaunin yankin
'Yan sanda sun tabbatar da harin
Rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce adadin mutanen da aka sace mutum biyar ne.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun fara aikin ceto, tare da nuna kwarin gwiwar samun nasara.
"A halin yanzu jami’anmu suna kan aikin ceto, kuma nan ba da jimawa ba za ku ji labarin nasara.”
"Yan bindigan sun shiga al’ummar Fananawa, suka kashe mutum ɗaya, suka sace biyar, sannan suka jikkata mutum ɗaya."

Kara karanta wannan
Ba a gama murnar cin zabe ba, yan ta'adda sun sace mataimakin ciyaman da kansiloli 2
"Muna yin duk mai yiwuwa domin ceto waɗanda aka sace tare da gurfanar da masu aikata laifin a gaban shari’a.”
- DSP Yazid Abubakar

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Zamfara: Shaidanin dan bindiga, Isihu Buzu ya halaka bayan guntule masa kai
- 'Yan bindiga sun kashe basarake, sannan sun sace tsohon jami'in Kwastam
- Mutane sun zo wuya, sun kama 'dan bindiga sun yanke masa hukunci a tsakiyar gari
- 'Yan bindiga sun kai hari Kano cikin dare, sun sace wani adadi na mutane
'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki wani wurin da ake hakar ma'adanai a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun aikata wannan danyen aiki ne a wani ramin hakar ma'adanai da ke garin Ratoso Fan, a karamar hukumar Barkin Ladi.
Majiyoyi sun bayyana cewa daga zuwan 'yan ta'addan, ba su yi wata-wata ba suka bude wa masu hakar ma'adanan wuta.
Asali: Legit.ng
