Za a Saki Wasu Bayanai kan Abubuwan da Suka Faru a Mulkin Buhari a Najeriya

Za a Saki Wasu Bayanai kan Abubuwan da Suka Faru a Mulkin Buhari a Najeriya

  • Tsohon hadimin Farfesa Yemi Osinbajo zai kaddamar da wani littafi wanda ya kunshi hakikanin abin da ya faru a mulkin Muhammadu Buhari
  • Ojudu, wanda ya yi aiki a ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya soki littafin da aka kaddamar kwanan nan kan rayuwar Buhari
  • Ya kuma yi watsi da batun cewa Buhari bai goyi bayan takarar Yemi Osinbajo a zaben fitar da gwanin jam'iyyar APC ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Mai Ba Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Shawara kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ojudu ya shirya wallafa littafi kan mulkin Marigayi Muhammadu Buhari.

Ojudo, Tsohon Sanatan Ekiti ta Tsakiya ya bayyana cewa littafin zai yi bayani dalla-dalla kan shekaru takwas na mulkin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Tsohon hadimin Osinbajo ya soki littafin Omole

Kara karanta wannan

'Ba Tinubu ba ne,' An ji wanda Buhari ya so ya zama dan takarar APC a zaben 2023

Leadership ta ruwiato cewa tsohon hadimin mataimakin shugaban kasar ya fadi haka ne yayin da yake martani kan littafin da aka wallafa kwanan nan a fadar Aso Rock.

Ojudu ya soki wannan littafin wanda Dr Charles Omole ya wallafa mai taken “From Soldier to Statesman – The Legacy of Muhammadu Buhari."

Sanatan ya ce littafinsa, wanda ke kan hanyarsa ta fitowa, zai ƙunshi hakikanin abin da ya faru a lokacin mulkin Buhari, bisa la’akari da rawar da ya taka a cikin gwamnatin da kuma ƙwarewarsa ta aiki.

Za a kara sakin bayanai kan mulkin Buhari

Ojudu ya ce:

"Bayanan da na rubuta game da shekaru takwas na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari za su fito nan ba da jimawa ba.
“Na yi niyyar gayyatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, zuwa wajen ƙaddamar da littafin. Ina kuma fatan za a ba ni damar gudanar da taron a Fadar Shugaban Ƙasa.”

Ya kara da cewa duba da yadda aka ba wani dama ya kaddamar da littafi a fadar shugaban kasa, shi ma ya kamata a matsayinsa na dan Najeriya a ba shi irin wannan dama.

Kara karanta wannan

"Yana sane": Diyar Buhari ta fadi halin marigayin da 'yan Najeriya ba su sani ba

Ya kuma bayyana cewa abin da ke kunshe a littafin Omole, bai yiwa rayuwar marigayi Buhari da gudummuwar da ya bayar adalci ba.

Buhari ya goyi bayan Osinbajo a 2022?

Ojudu ya kuma yi tsokaci kan abin da ya kira rashin daidaito a cikin bayanan da Omole ya gabatar dangane da zargin cewa Buhari bai goyi bayan Farfesa Yemi Osinbajo ba a zaɓen fidda gwani na APC na 2022.

Muhammadu Buhari.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari lokacin yana kan mulki Hoto: @MBuhari
Source: Facebook

Yayin da littafin Omole ya nuna cewa Buhari ya kaurace wa goyon bayan Osinbajo ne saboda alaƙarsa da Bola Tinubu, Ojudu ya musanta hakan.

Ya bayyana cewa marigayi Buhari ya nuna cikakken goyon baya da amincewa da Osinbajo a lokuta da dama, a bainar jama’a da kuma a tarurruka na sirri.

El-Rufai ya nemai a bar Buhari ya huta

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bukaci a bar marigayi Muhammadu Buhari ya huta a kabarinsa ba tare da maganganu a kansa ba.

Ya yi gargadi game da kokarin tayar da rikici, rarrabuwar kai ko anfani da tarihinsa don cimma wasu bukatun siyasa da jawo maganganu a tsakanin 'yan Najeriya.

El-Rufa’i ya ce taron kaddamar da littafi a kan tsohon Shugaban Kasa ya tayar masa da hankali, ganin yadda aka sake nuna rabuwar kai da ke kewaye da Buhari tun yana raye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262