‘Trump Bai San Najeriya ba’: Tambuwal Ya Fadawa Amurka Abin da ba Ta Sani ba

‘Trump Bai San Najeriya ba’: Tambuwal Ya Fadawa Amurka Abin da ba Ta Sani ba

  • Tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Aminu Tambuwal, ya yi tsokaci game da karuwar ta'addanci a Najeriya da maganar Amurka
  • Tambuwal ya ce ‘yan ta’adda ba sa wakiltar kowace addini, illa masu aikata laifuka ne da ke kashe al'umma
  • Tsohon gwamnan Sokoto ya bayyana halin tsaro a Najeriya a matsayin abin tayar da hankali, yana gargadin shugabanni

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya magantu kan matsalar tsaro.

Tambuwal ya ce ‘yan ta’adda ba sa girmamawa ko wakiltar kowace addini, yana mai jaddada cewa kawai makiyan al’umma ne da ke neman inda za su kai hari.

Tambuwal ya soki Trump kan zargin kisan Kiristoci
Tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media Office.
Source: Facebook

Tambuwal ya ci gyaran Trump kan kisan Kiristoci

Tsohon gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin tattaunawa da manema labarai a Sokoto a jiya Asabar 20 ga watan Disambar 2025, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Babu tausayi': Tinubu ya kuma yin albishir ga 'yan Najeriya game da ta'addanci

Ya bayyana cewa mutanen da ke aikata laifuka a sassan kasar nan ’yan ta’adda ne na gari, suna yaki da ’yan kasa ba tare da bambancin addini ba.

Tambuwal ya bayyana halin tsaro a Najeriya a matsayin “mai matuƙar tayar da hankali da firgici,” inda ya gargadi shugabannin siyasa da kuma al’ummar duniya da su guji mayar da tabarbarewar tsaro batun siyasa.

Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin takaici, yana mai cewa bai nuna ainihin yanayin matsalolin tsaron Najeriya da rikicinsu ba.

Tambuwal ya ce:

“Na yi imani Shugaba Trump da gwamnatin Amurka ba su fahimci ainihin halin da Najeriya ke ciki ba. Abin da muke fuskanta ba rikicin addini ba ne, rikicin tsaro ne da ke shafar ’yan Najeriya na kowane addini da asali.
“Waɗannan barayin ba sa wakiltar kowace addini. Ta yaya za a bayyana abin da suke yi a Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi da sauran jihohi? ’Yan ta’adda ne na gari, suna kai hari ga duk wanda suka ci karo da shi.
“Ba za ka iya zuwa masallaci ko coci cikin kwanciyar hankali ba. Don haka wannan ba batun wani yanki ko wani addini ba ne. Batun Najeriya ne gaba ɗaya."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi alkawarin da ya yi wa Amurka da Turai kan tsaron Najeriya

Tambuwal ya kalubalanci Trump kan kisan Kiristoci a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Kisan Kiristoci: Tambuwal ya yabawa fadar Vatican

Tsohon gwamnan ya goyi bayan matsayar Fadar Vatican, yana mai cewa Fafaroma ya yi daidai wajen amincewa Kiristoci da Musulmi a Najeriya duka suna fama da matsalar tsaro.

Tambuwal ya jaddada cewa rashin tsaro ya zama matsalar ƙasa baki ɗaya, wadda ta wuce siyasa, kabila da addini, yana mai cewa akwai buƙatar haɗin kai cikin gaggawa.

Ya bukaci Amurka da sauran ƙawayen duniya su sake duba matsayarsu, tare da tallafa wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin shawo kan matsalar, cewar Daily Post.

Tambuwal ya fadi matsalar Tinubu a mulki

A baya, an ji cewa tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya soki shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa.

Tambuwal yana zargin gwamnatin Tinubu da APC da rashin sanin tsarin mulki da yadda ake tafiyar da Najeriya.

Sanata Tambuwal ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya fi Tinubu fahimtar mulki, musamman a batun tsarin mulkin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.