APC Ta Yi Babban Rashi, Jigonta kuma Tsohon Kwamishina Yar Bar Duniya
- An tafka babban rashi bayan sanar da rasuwar jigon jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda ya ba al'umma gudunmawa
- An tabbatar da rasuwar tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Edo, Charles Idahosa wanda ya rasu yana da shekaru 72
- Idahosa ya taka rawar gani a siyasar Edo, inda ya yi aiki tare da Oshiomhole, Obaseki, sannan ya koma APC kafin rasuwarsa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Benin - Jam'iyyar APC ta tafka babban rashin daya daga cikin jiga-jiganta wanda ya ba al'umma gudunmawa.
Tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Edo kuma jigo a jam'iyyar mai mulkin Najeriya, Charles Idahosa, ya rasu yana da shekaru 72.

Source: Twitter
Tsohon kwamishina a Edo ya bar duniya
Hakan na cikin wani sako da wani makusancin iyalan marigayin ya bayyana cikin alhini da mayar da lamura ga Allah da jaridar Vanguard ta samu.
Mutumin ya ce sun samu labarin rasuwar wacce ta zo a bazata duba da cewa marigayin yana da karfinsa da kuzari da safiyar ranar.
Ya ce:
“Baba yana cike da kuzari da safe, kamar yadda ya saba, ya sauko ƙasa yana karɓar baƙi. Ban san abin da ya faru ba, abin ya ba mu mamaki sosai.”
Marigayin ya yi aiki a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Edo, Lucky Igbinedion.
Charles Idahosa, wanda aka fi sani da laƙabin Akakasiaka da Charlie Tempo, ya shahara wajen faɗar albarkacin bakinsa a harkar siyasa.
Ya kasance mai ba Adams Oshiomhole shawara kan harkokin siyasa tsawon shekaru takwas da ya yi a matsayin Gwamnan Edo, cewar rahoton The Nation.
Daga bisani, Idahosa ya mara wa Godwin Obaseki baya bayan rikicin siyasa da ya shiga tsakaninsa da Oshiomhole, har ma ya wallafa wani littafi mai taken “The Fall of the Last Godfather”.

Source: Original
Tarihin siyasar marigayi jigon APC, Idahosa
A shekarar 2020, marigayin ya bi Obaseki zuwa jam’iyyar PDP amma daga baya sun samu sabani bayan sake zaɓen Obaseki a wa’adi na biyu.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Malami ya yi sababbin zarge zarge kan shugaban EFCC bayan ci gaba da tsare shi
Idahosa ya kasance ɗaya daga cikin ’yan siyasar farko da suka fito fili suka bayyana rashin jituwarsu da Obaseki bayan zaɓen, inda daga bisani ya koma jam’iyyar APC.
Haka kuma, shi ne ɗaya daga cikin na farko da suka fitar da wakokin kamfe domin goyon bayan zaɓen Gwamnan Edo na yanzu, Monday Okpebholo.
Rasuwar Charles Idahosa ta bar babban gibi a siyasar Jihar Edo, inda abokan siyasa da magoya baya ke bayyana alhininsu kan mutuwar wannan gogaggen ɗan siyasa.
An sanar da rasuwar tsohon Sanata
An ji cewa Gwamnatin jihar Delta da ke Kudancin Najeriya ta tura sakon ta'aziyya game da mutuwar tsohon Sanata da ya yi bankwana da duniya.
Rasuwar Sanatan wanda ya wakilci Delta ta Arewa, Peter Nwaoboshi ya jefa al’ummar Anioma, Delta da Najeriya cikin alhini.
Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, yana yabawa jajircewar Nwaoboshi wajen kare muradun Anioma.
Asali: Legit.ng
