Abin da Tinubu Ya Fada a Gidan Dahiru Bauchi bayan Saka Wa Jami’a Sunansa

Abin da Tinubu Ya Fada a Gidan Dahiru Bauchi bayan Saka Wa Jami’a Sunansa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan jami'ar tarayya guda da ke Azare zuwa sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi
  • Tinubu ya ce ya yi hakan ne domin girmamawa da kuma dawwamar da tarihin fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi
  • Gwamna Bala Mohammed da iyalan marigayi malamin sun yaba da wannan mataki, suna cewa ya nuna girman gudunmawar da ya bayar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi bayan rasuwarsa a watan Nuwambar 2025.

Tinubu ya shiga jihar Bauchi ne domin jaje ga iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya rasu a ranar 27 ga watan Nuwambar 2025.

Abin ya sa Tinubu ya karrama Dahiru Bauchi
Bola Tinubu da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Source: Twitter

Yadda Tinubu ya karrama marigayi Dahiru Bauchi

Tinubu ya sanar da wannan mataki ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalan marigayin a gidansa da ke Bauchi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rada wa babbar jami'a a Najeriya sunan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Shugaba Tinubu ya yi hakan ne domin girmama fitaccen malamin Musulunci da ya rasu duba da gudunmawar da ya ba addini.

A cewar Tinubu, an sauya sunan jami’ar ne domin yaba marigayin a bangaren tarihi tare da girmama gudunmawarsa ga bil’adama da kuma ilimin addinin Musulunci.

Ya ce:

“Daga yau, na sanar da wannan sauyin suna domin a dawwamar da gudunmawar da ya bayar. Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Lafiya, Azare, daga yau za a rika kiranta da Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Allah ya yi masa rahama.”

Shugaban ya ce rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin babban rashi, yana mai cewa rayuwar malamin ta kasance cike da tawali’u, hidima ba tare da son kai ba, da kuma jajircewa wajen yaɗa Musulunci da zaman lafiya.

Har ila yau, Shugaban ya yi addu’ar Allah ya ba iyalan marigayin, gwamnatin jihar Bauchi da al’ummar jihar, ƙarfin zuciya da juriyar jure wannan babban rashi, tare da kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da addu’ar zaman lafiya da haɗin kai a ƙasa.

Iyalan Dahiru Bauchi sun yi godiya ga Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Martanin iyalan Sheikh Dahiru Bauchi ga Tinubu

Kara karanta wannan

An sanya dokoki a gari saboda ziyarar da Bola Tinubu zai kai gidan Sheikh Dahiru Bauchi

Da yake mayar da martani a madadin iyalan marigayin, babban ɗansa, Sheikh Ibrahim Usman Bauchi, ya gode wa Tinubu bisa ziyarar ta’aziyya, addu’o’i da kuma girmamawar da ya yi wa mahaifinsu.

Ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, bisa irin goyon bayan da yake bai wa iyalan tun bayan rasuwar marigayin, kamar yadda ya wallafa a Facebook.

A jawabinsa, Gwamna Bala Mohammed ya godiya ga Tinubu bisa karramawa da ya yi wa Bauchi da iyalan Sheikh Dahiru Bauchi, yana mai cewa hakan wata shaida ce ta gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar ga addini.

UNIMAID: Tinubu ya karrama marigayi Buhari

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa 'Muhammadu Buhari University', a matsayin girmamawa.

Tinubu ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, wanda bai yarda da son rai ko hauragiyar siyasa marasa tushe ba.

Shugaban ya bayyana cewa Buhari ya kafa tsari na gaskiya da rikon amana da zai ci gaba da zama madubi ga shugabannin gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.